KannyWood

Ƙungiyar ‘Kannywood Family’ ta Shirya Gagarumin Bikin Karrama Gwarazan Kannywood

Bikin Karrama Gwarazan Kannywood – Legendary Award Night 2025

Kannywood Family Group ta shirya bikin gagarumin inda zata karrama gwarazan Kannywood maza da mata. Bikin, wanda aka yi wa laƙabi da “Legendary Award Night”, za a gudanar da shi a ranar Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025 da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, a ɗakin taro na otal ɗin The Afficent, Magaji Rumfa, Kano.

Manufar Bikin

An shirya taron ne domin:
✅ Sada zumunci da haɗa kan juna
✅ Ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a masana’antar Kannywood
✅ Girmama gwarazan da suka taka rawar gani

Kwamitocin da Za Su Jagoranci Bikin

An kafa kwamitoci daban-daban don tabbatar da ingantaccen shiri:

🔹 Kwamitin Karɓar Baƙi: Hauwa Waraka, Fati Muhammad, Esha Golden, da Nura MC Khan.
🔹 Kwamitin Walwala: Hadiza Maikano, Danja, Fati Al-Amin, da Maijidda Abbas.
🔹 Kwamitin Tsaro: Halisa Muhammad, Waziri Godowoli, da Kalambaina Ikon Allah.
🔹 Kwamitin ‘Yan Jarida: Mujallar Fim, Abba Pash, Sadamcy Photography, da sauran bloggers.
🔹 Kwamitin Tattara Bayanai Kan Waɗanda Suka Rasu: Hajiya Fatima, Hajiya Maryam CTV, Hajiya Zulai Bebeji, Hajiya Asma’u, Hafsat Suleiman, da Fati Suleiman.

Gayyatar Jama’a

Shugabannin taron sun bayyana cewa ƙofar taron a buɗe take ga duk masu sha’awar ba da shawara da gudunmawa. Haka kuma, katin gayyata yana hannun furodusa Yakubu Gwammaja. Duk wanda yake bukata zai iya karɓa a wurinsa.

Ana maraba da duk wani ɗan Kannywood—babu wanda aka ware!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button