Labaran Duniya

Shugabannin Larabawa sun gudanar da taron gaggawa a Qatar kan harin Isra’ila

Taron Gaggawa a Qatar kan Harin Isra’ila

A yau shugabannin kasashen Larabawa sun gudanar da taron gaggawa a birnin Doha, Qatar, domin mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labarai Reuters ya ruwaito cewa taron ya fi karkata ne kan kisan kiyashi, yunwa da azabtar da fararen hula da Isra’ila ke yi, lamarin da ke barazana ga zaman lafiya da ci gaban Larabawa.

Shugabannin sun hallara domin nuna cikakken goyon baya ga Qatar, wadda ta yi Allah wadai da harin da aka kai mata.

A gefe guda, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Qatar babbar abokiyar Amurka ce, don haka ya ja hankalin Isra’ila da ta rika yin taka tsantsan kafin kai duk wani hari a nan gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks