KannyWood

“Na Iya Girki, Kuma Ina Da Saurin Hadda Script – A’isha Humaira”

Jarumar fina-finan Hausa, A’isha Humaira, ta bayyana wasu daga cikin basirorinta yayin wata hira da ta yi da shirin Sirrin Daukaka na DCL Hausa. A cewarta, tana da kwarewa sosai wajen girki, duk da cewa ba ta yin hakan don kasuwanci.

Ta ce girkin da take yi yana matukar burge mutane a gida da wajen gidanta, kuma tana jin dadin hakan a matsayin wani bangare na rayuwarta.

Baya ga iya girki, A’isha Humaira ta bayyana wata dabara da take da ita wadda ta bambanta ta da sauran jarumai. Ta ce tana da saurin haddace “script” na fina-finai, wanda hakan ke sa ta gudanar da aikinta cikin sauki da kwarewa.

Ta kara da cewa wannan basira da take da ita tana taimaka mata wajen shigewa cikin kowanne irin matsayi da ake bukata a fim, cikin kankanin lokaci, ba tare da jinkiri ba. Wannan na daga cikin sirrin nasararta a harkar fim.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button