Wasanni

“Ban ji haushi ba” – Mbappe ya bayyana bayan PSG ta lashe Champions League

Kylian Mbappe ya bayyana cewa bai ji wani haushi ba dangane da yadda tsohuwar kungiyarsa ta Paris Saint-Germain (PSG) ta lashe gasar Champions League, shekara guda bayan barinsa zuwa Real Madrid.

Mbappe, wanda ya bar PSG a matsayin jagoran cin kwallaye na tarihi da kwallaye 256, bai samu damar daukar kofin Champions League ba duk da shekaru bakwai da ya shafe a kungiyar. A watan Yuli na bara ne ya koma Real Madrid a matsayin dan wasa mara kwangila.

PSG ta lashe kofin ne bayan ta doke Inter Milan da ci 5-0 a wasan karshe da aka buga a filin wasa na Munich Arena a Jamus, ranar 31 ga watan Mayu.

“Ban bar kungiyar da wuri ba. Tarihina da PSG ya zo karshe ne. Ba na jin haushi ko nadama. Na san na bayar da duk abinda nake da shi,” in ji kyaftin din tawagar Faransa, yayin da yake jawabi ga manema labarai gabanin karawar Faransa da Jamus a gasar UEFA Nations League.

Ya ci gaba da cewa:

“Allah ya kaddara cewa su ne za su lashe kofin – ba tare da ni ba. Amma ni farin ciki nake. Sun cancanci nasarar.”

Mbappe ya jaddada cewa kungiyar ta fuskanci kalubale da yawa tsawon shekaru, ciki har da lokacin da yake cikinta:

“Na taka leda a kowane mataki na gasar tare da PSG – in ban da wannan matakin na nasara. Ban taɓa ganin ƙungiyar da ta doke abokan karawa da ci 5-0 a wasan karshe ba. Wannan babban abu ne.”

A shekarar 2020 ne PSG ta kusan lashe Champions League, amma ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Bayern Munich a wasan karshe – wannan shi ne mafi kusa da nasara da Mbappe ya taba kai wa tare da kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button