Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

Lamine Yamal Ya Bayyana Shakku Kan Lashe Ballon d’Or
Matashin tauraron Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ba ya da tabbacin lashe kyautar Ballon d’Or na bana. Ya ce akwai ‘yan wasa da dama da suka fi cancantar lashe kyautar a wannan shekarar.
A kakar wasa ta 2024/25, Yamal ya taka gagarumar rawa wajen taimaka wa Barcelona ta lashe manyan kofuna uku:
- La Liga,
- Copa del Rey,
- Supercopa de España.
Duk da haka, a wata hira da aka yi da shi a shirin El Partidazo de COPE, Yamal ya ce burinsa na lashe Ballon d’Or zai fi yuwuwa ne idan har ya taimaka wa kasarsa ta Sifaniya wajen lashe:
- Gasar Zakarun Turai (UEFA Euro) da
- Kofin Duniya (FIFA World Cup).
“Ba na yawan tunani a kai. Idan na fara sa wa a raina cewa dole sai na lashe Ballon d’Or, hakan zai iya jefa ni cikin matsala. A yanzu ina mayar da hankali ne kan wasan da nake yi. Wata rana in Allah ya so, kyautar za ta zo,” in ji Yamal.
“Idan muka lashe gasar zakarun Turai da kuma kofin duniya a shekara mai zuwa, to akwai yiyuwar in samu Ballon d’Or. Amma a yanzu dai, ban sa ran hakan ba,” ya ƙara da cewa.