Ba Don Tarbiyantar Da Mutane Nake Yin Fim Ba -Amina Shehu Lulu

Amina Shehu Lulu (Sabuwar Zeezee) Ta Bayyana Gaskiya Kan Rayuwarta da Harkar Fim
Amina Shehu Lulu, wadda wasu ke kira Sabuwar Zeezee, ta yi karin haske kan dalilin da ya sa ta shiga harkar fim da kuma ra’ayinta game da yadda mutane ke kallon jaruman Kannywood.
A wata hira da ta yi da DW Hausa, Lulu ta bayyana cewa asalin ta yar Zariya ce, Jihar Kaduna, amma ta yi karatu har ta kai Jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Dalilin Shigarta Fim
A cewar Lulu:
“Ba wani abu ya sa na shiga harkar fim ba face kasuwanci. Ni ba na yin fim don koyar da tarbiyya ko bata tarbiyya. Ina yi ne domin na samu abin rufawa kaina asiri. Bayan fim, ina da sana’o’in kasuwanci da nake yi don neman kudi. Ni yar kasuwa ce, ba malamar tarbiyya ba.”
Ba Ta So A Kwaikwayi Rayuwarta
Lulu ta jaddada cewa ba ta da wani nadama kan kasancewarta jaruma, amma ta ja hankalin jama’a cewa kada su dauke ta a matsayin abin kwaikwayo:
“Ni mutum ce kamar kowa. Ina yin kuskure, ina yin daidai. Ba na so a ce dole kowa ya yi abinda nake yi. Ba lallai ba ne duk abinda nake yi ya burge mutane. Idan ka kwaikwayi wani abu daga gareni, kai ka ga dama. Ba zan yi wani abu don gyara ko bata tarbiyyar wani ba.”
Burinta A Masana’antar Nishadi
Daga karshe, Lulu ta bayyana burinta na daina fim kafin ta tsufa:
“Ba na fatan in yi shekaru fiye da goma a masana’antar nan. Ina son in ba matasa masu tasowa dama. Bana so in jira sai na tsufa kafin a daina dora mani kyamara.”
Amina Shehu Lulu ta bude zuciyarta ga jama’a ta hanyar bayyana gaskiyar rayuwarta da dalilinta na harkar fim. Ta nuna cewa ba ta da burin zama abin kwaikwayo, domin ita ma mutum ce kamar kowa.