Abin Da Ya Sa Na Yi Batan Dabo A Kannywood – Zainab Indomie

Zainab Abdullahi, wadda aka fi sani da Zainab Indomie, na daga cikin fitattun taurarin Kannywood da suka yi fice a baya a masana’antar fina-finan Hausa.
Tsohuwar jarumar ta yi fice a Kannywood ne sakamakon yadda ta iya taka rawa a matsayi iri-iri, tare da ƙwarewa wajen kwalliya da kuma yadda muryarta ke jan hankalin masu kallon fina-finai a lokacin.
Yayin da taurarta ke ci gaba da haskawa a masana’antar, kwatsam sai aka daina jin ɗuriyarta, lamarin da ya jefa masoyanta cikin tambaya kan inda ta shige.
Sai dai a cikin shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, Zainab ta bayyana dalilan da suka sa ta ɓace daga fagen fina-finai da kuma inda take yanzu.
A cewarta, ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa ta fice daga Kannywood shi ne lokaci ne ya yi na bayar da dama ga sabbin fuska.
“Hausawa suna cewa: ‘Sai an matsa, sannan wani zai samu wuri.’ Idan wanda ke kan wuri ya ƙi matsawa, na bayansa ba za su samu damar hawa ba,” in ji Zainab Indomie.
“Idan mutum ya samu nasara a lokacin sa, ya kamata ya bar wa wasu dama su yi fice a zamaninsu,” ta ƙara da cewa.
A baya an taɗa jita-jitar cewa Zainab ta shiga cikin wasu gungun mutane da ake zargi da ɓata tarbiyya.
Sai dai jarumar ta karyata wannan zargi, tana mai bayyana cewa labarin ba shi da tushe ko sahihanci.
Ta jaddada cewa dalilin ɓoyewarta shi ne kawai cikar lokacin ta a Kannywood, ba wani dalili na ɓata suna ba.