Nigeria

Gwamnatin Katsina Ta Ce Tallafin Da Ta Baiwa Yan Bindiga Da Suka Tuba Zai Rage Matsalar Tsaro

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa matakin tallafawa Yan bindiga da suka tuba ya samo asali ne daga bukatar magance manyan dalilan da suka jefa su cikin aikata laifi, musamman rashin ilimi da rashin aikin yi.

A cewar gwamnati, waɗannan dalilai ne suka taka muhimmiyar rawa wajen haifar da matsalar tsaro da jihar ke fama da ita.

Kwamishinan tsaro na jihar, Dokta Nasiru Matazu, ya bayyana cewa Yan bindiga da suka tuba suka mika wuya sun roki gwamnati ta samar musu da makarantu domin ƙara ilimantar da yaransu, asibitoci don kula da lafiyarsu, da kuma wuraren shan ruwa ga shanunsu.

Ya ce samar da waɗannan abubuwa zai taimaka wajen tabbatar da cewa masu laifin da suka tuba ba za su koma ga munanan ayyukan baya ba.

See also  TIN a Najeriya: Yadda Ake Samunta, Muhimmanci da Tasirin Dokar Haraji 2026

Sai dai masana harkokin tsaro sun yi jan hankali, suna cewa bai kamata a mayar da hankali ga tallafawa ƴan bindiga kawai ba.

Dokta Kabiru Adamu, ƙwararre a fannin tsaro, ya bayyana cewa ya kamata a fi karkatar da irin wannan tallafi zuwa ga al’ummomin da matsalar ta shafa kai tsaye.

A cewarsa, akwai al’ummomin da suka rasa shanu, dukiyoyi, da ‘yan uwa sakamakon hare-haren ƴan bindiga, don haka su ne suka fi bukatar tallafin gwamnati.

Ya kuma yi gargadi cewa rarraba tallafi kai tsaye ga ƴan bindiga na iya ƙara musu ƙwarin guiwa, har ma ya zama kamar an ba su lada saboda aikata laifi.

See also  Janar Christopher Musa ya shawarci ’yan Najeriya su koyi dabarun kare kai

“Ba duka yan bindigan suka shiga ne saboda ƙuncin rayuwa ba. A cikinsu akwai waɗanda suka mayar da sata da garkuwa da mutane sana’a,” in ji shi.

Matakin gwamnatin Katsina na zuwa ne bayan wasu al’ummomin jihar sun shiga tattaunawar sulhu da yan bindiga.

Duk da haka, rahotanni sun nuna cewa sulhun bai dakatar da hare-haren yan bindiga a wasu jihohin da ke makwabtaka da Katsina ba, inda har yanzu ake fuskantar matsaloli na tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks