Ademola Lookman, ɗan wasan gaba ɗan asalin Najeriya, zai ci gaba da zama a Atalanta duk da ƙoƙarin Inter Milan na ɗaukar sa a wannan bazarar canjin ‘yan wasa.
An kawo ƙarshen takaddamar da aka kwashe makonni ana yi tsakanin Atalanta da Inter Milan, bayan da tayin dala miliyan 53 da Inter ta miƙa aka ƙi amsawa. Wannan ya sa a ƙarshe cinikin ya rushe.
Lookman, wanda ya buga wa Atalanta ƙwallaye 20 a kakar da ta gabata a dukkan gasa, ya koma atisaye tare da ‘yan uwansa karkashin sabon koci Ivan Juric, bayan dawowarsa daga buga wasanni da tawagar Super Eagles ta Najeriya.
A watan Agusta, alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da Atalanta, inda har ya goge hotunan ƙungiyar daga shafukan sada zumunta.
Sai dai yanzu ya amince da ci gaba da taka leda a Bergamo, lamarin da ya nuna kwarin gwiwar Atalanta wajen ƙin rabuwa da fitattun ‘yan wasanta na gaba.
Za a jira ganin ko Ademola Lookman zai iya mantawa da wannan rikici tare da taya Atalanta fafutukar neman kofuna a kakar Serie A ta bana.


















