Ballon d’Or 2025: Wa zai lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa?

A yau Litinin, 22 ga Satumba 2025, za a karrama gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na duniya ta maza da mata a bikin Ballon d’Or da ake gudanarwa a Theatre du Chatelet, birnin Paris, Faransa.
Ana karrama waɗanda suka fi nuna bajinta a kakar bara, inda aka zaɓi jerin ‘yan wasa 30 da suka cancanci lashe kyautar. Daga cikin jerin, za a bayyana wanda ya fi kwazo a maza da kuma na mata, sannan a jera sauran daga na biyu har zuwa na 30.
BBC ta rairayo manyan ‘yan ƙwallo biyar da ake ganin suna kan gaba a wannan shekarar.
Ousmane Dembele (Paris Saint-Germain)

- Ya buga wasa 53, minti 3,483
- Ya zura ƙwallo 35, ya taimaka aka ci 14
- Ya taimaka wa PSG ta lashe Ligue 1 da Champions League karo na farko a tarihinta
- Ya zura ƙwallo 21 a Ligue 1, inda ya zama gwarzon gasar
- A Champions League, ya ci 8, ya taimaka 6
- Ya ci kwallo a wasannin ƙungiyoyi na duniya da Bayern Munich da Real Madrid
Raphinha (Barcelona)

- Ya buga wasa 57, minti 4,661
- Ya zura ƙwallo 34, ya taimaka aka ci 22
- Ya taimaka wa Barcelona ta lashe La Liga, Copa del Rey, Supercopa de Espana
- Ya ci 18 a La Liga, inda ya zama gwarzon gasar
- Ya zura ƙwallo 13 a Champions League, ciki har da uku rigis a Bayern Munich
Harry Kane (Bayern Munich)

- Ya buga wasa 51, minti 3,955
- Ya zura ƙwallo 41, ya taimaka aka ci 12
- Wannan ne kofinsa na farko a tarihin kwallon ƙafa
- Ya ci ƙwallo 26 a Bundesliga, ciki har da hat-trick sau uku
- A watan Satumba kawai ya zura ƙwallo 10 a kwana 11, ciki har da huɗu a wasan Dinamo Zagreb
Kylian Mbappe (Real Madrid)

- Ya buga wasa 59, minti 4,742
- Ya zura ƙwallo 44, ya taimaka aka ci 5
- Ya ci 31 a La Liga, inda ya zama gwarzon gasar
- Ya ci hat-trick a ragar Barcelona, sannan ya cire Man City daga Champions League
- Ya zama ɗan wasa na uku a tarihin Faransa da ya kai ƙwallaye 50
Lamine Yamal (Barcelona)

- Ya buga wasa 55, minti 4,548
- Ya zura ƙwallo 18, ya taimaka aka ci 21
- Ya taimaka Barcelona ta lashe kofuna uku
- Ya lashe gwarzon ɗan wasa na La Liga a watan Satumba
- Ya ci ƙwallo biyu a wasan Spain da Faransa a kusa da ƙarshe
Duk da cewa jerin sun cika da ‘yan kwallo masu bajinta, kwararru na ganin Mbappe, Dembele da Raphinha ne suka fi yin tasiri a kakar da ta gabata. Sai dai har yanzu ana jiran sakamakon ƙarshe wanda zai nuna wanene ya fi cancanta lashe kyautar Ballon d’Or 2025.