JARUMA Rayya ta yi tambaya kan yadda mutane za su ji idan ta zana Tattoo, lamarin da ya jawo ‘yan Kannywood da dama suka yi martani. Shugaban hukumar fina-finan Najeriya, Ali Nuhu, ya gargade ta da cewa:
“Ke! Kar ki soma wallahi. Bulalar nan tana nan ban jefar da ita ba.”
Tambayar Rayya a shafinta na Instagram ta jawo cece-ku-ce daga abokan sana’a da masoyanta, ciki har da waÉ—annan martanin:
Madam korede: “Wallahi za ki kara kyau Rayyah dan kaniyanki.”
Officialzeezango_: “Kar ki yi gaskiya.”
Nasirualikoki1: “Ki rufa mana asiri.”
nazir_danhajiya: “Zan zane ki har sai kin yi kuka.”
Wasu daga cikin shugabannin masana’antar Kannywood da masoya sun nuna rashin amincewarsu kan wannan yunkuri, suna mai cewa bai dace ba.

























