Amaryar TikTok Ta Fadi Matsalar da Jaruman Kannywood ke Fuskanta

Hafsat Tuge, wadda aka fi sani da Amaryar TikTok, ta ce mutane suna kallon ‘yan fim mata da wani kuskuren fahimta. Ta ce ana ganin kamar ba su dace da aure ba, amma wannan ba gaskiya ba ne.
A cewarta, yawancin ‘yan fim mata suna aure. Suna girmama mazajensu kamar kowace mace. Ta ce mutane ne kawai ke musu kallon daban saboda su ‘yan fim ne, suna samun kuÉ—i, kuma suna aiki da maza. Amma hakan bai nufin ba su da tarbiyya ba.
“Aure ba ya gabana yanzu” – Hafsat Tuge
Da aka tambayi Hafsat lokacin da za ta yi aure, ta ce aure yana da lokaci. “Zan yi aure idan lokacin ya yi. Amma yanzu ba shi ne a gabana ba,” in ji ta.
Fim ba gaskiya ba ne
Wasu na zargin ‘yan fim da lalata tarbiyya. Amma Hafsat ta ce, “Fim ba gaskiya ba ne. Idan ka É—auki abin da aka yi a fim da gaske, to kana cikin matsala.”
Daukaka daga Allah ke zuwa
Hafsat ta ce ba lallai mutum ya samu daukaka saboda yana da ubangida ba. Wasu sun daukaka ba tare da dogaro da kowa ba. Amma wasu sun samu tallafi ne daga wani.
Ta bukaci hadin kai a Kannywood
A Æ™arshe, ta roÆ™i ‘yan fim su hada kai. Ta ce idan suka zama tsintsiya madaurinki daya, za su samu ci gaba a masana’antar.