Labaran Duniya

An Sanar da Ganin Jinjirin Watan Shawwal a Najeriya

An ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya a ranar Asabar, wanda ya sa masarautar ƙasar ta ayyana Lahadi, 30 ga watan Maris 2025, a matsayin ranar Sallah.

A shafin Facebook na Haramin, dandalin Musulmin duniya, an wallafa sanarwar cewa:

An ga jinjirin watan Shawwal 1446 a Saudiyya. Saboda haka za a yi Sallah gobe Lahadi, 30 ga watan Maris, 2025.”

Tun da farko a wannan Asabar, Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta buƙaci Musulmi su sanya ido don ganin watan.

A wata sanarwa da Farfesa Is-haq Oloyede, babban sakataren Majalisar, ya fitar, an shawarci Musulmi su sanya ido don ganin watan da zarar rana ta faɗi a wannan Asabar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button