Zaben APC 2027, Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa jam’iyyar APC mai mulki na iya fuskantar matsaloli iri ɗaya da suka addabi wasu tsofaffin jam’iyyun adawa a Najeriya, musamman dangane da rashin daidaito a cikin gida.
Wannan ra’ayi ya biyo bayan wasu kalamai daga ɓangaren tsohuwar jam’iyyar ANPP — ɗaya daga cikin jam’iyyun da suka haɗu suka kafa APC — inda suka nemi a bai wa ƴaƴansu damar samun kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Wasu daga cikin waɗanda suka fito daga ANPP sun bayyana bukatar ganin an bai wa tsoffin mambobin jam’iyyar guraben jagoranci a cikin gwamnatin APC. A cewarsu, ya kamata a ba su wakilci daidai da irin gudunmuwar da suka bayar tun kafuwar jam’iyyar a shekarar 2013.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, sun jaddada cewa bai kamata a manta da irin rawar da suka taka ba, tun daga kafa jam’iyyar har zuwa samun nasarar da APC ta samu a zaɓen 2015.
Sun kuma buƙaci hadin kai da adalci daga gwamnatin shugaba Bola Tinubu, tare da jan hankali cewa kamata ya yi a duba bukatunsu cikin hikima da fahimta, domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan jam’iyyar.


















