Nishadi

Amfanin Cin Kwai Ga Lafiyar Jiki: Abubuwa 7 da Ya Ke Yi a Jikin Dan Adam

Kwai abinci ne da kusan kowa ke ci a Najeriya, musamman da safe. Amma ka taɓa tambayar kanka me kwai ke yi a jikin mutum? A nan za mu bayyana amfanin cin kwai ga lafiya da kuma yadda ake cin sa cikin natsuwa.

1. Gina Jiki da Ƙarfafa Tsoka

Kwai na ɗauke da sinadaran protein masu yawa. Wannan na taimaka wajen ƙarfafa tsoka da kuma gyaran sassan jiki, musamman ga masu motsa jiki da matasa.

Ana samun kusan 6 grams na protein a cikin kowanne kwai.

2. Inganta Hankali da Ido

Kwai na ɗauke da sinadarai kamar choline da lutein, waɗanda ke taimakawa kwakwalwa da ido. Wannan na kara hankali da rage hadarin cutar makanta.

Yana da amfani musamman ga yara da tsofaffi.

3. Rage Kasadar Ciwon Zuciya

Kwai na dauke da HDL (good cholesterol) wanda ke taimakawa rage hadarin ciwon zuciya. Duk da cewa yana da cholesterol, kwai ba ya haddasa matsala idan ana ci daidai.

Likitoci na shawartar a ci kwai ɗaya zuwa biyu a rana.

4. Taimakawa Masu Son Rage Kiba

Cin kwai da safe na taimakawa wajen jin cikar ciki har zuwa rana. Wannan yana rage yawan cin abinci da kuma taimakawa wajen rage kiba cikin lafiya.

Masu son diet na amfani da kwai a matsayin breakfast.

5. Kariyar Fata da Gashi

Sinadaran cikin kwai kamar Biotin da Vitamin D na taimakawa wajen lafiya da kyalli na fata da kuma ƙarfafa gashi.

See also  "Na rage ƙiba ne domin lafiyar kaina, kuma ni a yanzu nafi jin daɗin rayuwa ta, lokacin da nake da ƙiba bana jin daɗin jikina ~ Cewar Jaruma Hadiza Gabon

6. Ƙarfafa Kashi da Hakora

Vitamin D da phosphorus cikin kwai na taimaka wa jiki ya sha calcium yadda ya kamata. Wannan na ƙarfafa kashi da rage hadarin fama da tsoka ko ciwon gabobi.

7. Sauƙin Samuwa da Sauƙin Daɗa shi Cikin Abinci

Ɗaya daga cikin manyan ribar kwai shi ne sauƙin samuwa da amfani da shi. Ana iya dafawa, soyawa, ko hada shi da salak da noodles.

Kwai abinci ne mai arha, mai saukin hadawa, amma cike da sinadarai masu amfani. Yana da kyau a ci shi akai-akai, amma cikin idai-idai — domin cin yawa ma ba daidai ba ne. Idan kana da wasu larura, ka tuntubi likita kafin ka fara cinshi kullum.

See also  Jamila labarina Ta Bayyana: "Ni Ban Da Alaƙa Da Gidan Sarauta"

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks