Labaran Duniya

Atiku Abubakar: Buhari Ya Sadaukar da Rayuwarsa Wajen Kishin Ƙasa

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin “mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen nuna kishin ƙasa da ƙarfafa haɗin kan Najeriya.”

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Atiku ya ce: “Najeriya ta yi babban rashi. Mun rasa dattijo wanda ya ɗauki nauyin shugabanci a lokutan tsoro da nasara. Sadaukarwarsa za ta ci gaba da zama abin tunawa.”

Atiku ya yi addu’a Allah ya gafarta wa Buhari, ya yafe masa kurakuransa, kuma ya saka masa da Aljannar Firdausi. Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da daukacin ‘yan Najeriya.

Duk da irin gogayya da hamayya da ta kasance tsakaninsu a lokuta daban-daban na takarar shugabancin ƙasa, musamman a zaɓen 2019, Atiku ya nuna girma da ɗaukaka wajen girmama mutuwar tsohon shugaban.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks