KannyWood

Hadiza Gabon Ta Ba ‘Yan Mata Shawara Kan Zabin Aure

Hadiza Gabon Ta Ba ‘Yan Mata Shawara Kan Zabin Aure

Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta shawarci ‘yan mata da su daina nacewa sai sun auri saurayinsu, a maimakon haka su duba kowanne miji da zai iya zama nagari, har da mazajen aure. Wannan shawara ta ja hankalin mutane da dama a dandalin sada zumunta.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Alhamis, jarumar ta bayyana ra’ayinta da cewa:
“Ba dole sai saurayinki ba, ko mijin wata kika samu ki aura.”

Hadiza ta ce wannan shawarar asali daga daraktan finafinan Hausa, Hassan Giggs, wanda ya tura mata sakon domin ta yada shi.

Ra’ayoyin Mutane Kan Shawarar Hadiza Gabon

Shawararta ta jawo martani daga masu bibiyarta, inda sama da mutane 7,500 suka nuna jin dadinsu, yayin da sama da mutane 450 suka yi tsokaci.

Ga wasu daga cikin martanin:

jiddarh_caps: “Wata ta aure min saurayi babu kunya bare tsoron Allah. Nima mijin wata zan aura, kowa ya ji babu dadi.”

shamciyer: “Gaya masu dai, ‘yar uwa. Mu dama mijin wata shi ne burinmu.”

harunmahammadt: “Allah ya kai haske kabarin El Mu’az. In dai naga kin dora wani abu na dariya, shi kawai nake tunawa. Allah ya sa mu hadu a Aljannah.”

haleemaah__: “Wai mijin wata? Ku ce mai mata kawai. Kuma kaddara ai duk wanda Allah ya tsara za ka aura shi ne mijinka. Allah ya ba mu nagari.”

Shawarwari Ga Mata

Wasu daga cikin masu tsokaci sun yi kira ga mata da su kula da mazajensu domin kar wata ta kwace su.

fatima_ummu: “To mata, ku kula da mazajenku. Dije tana fatawa, kar kuma a yi korafi a baya.”

incense.by.sadeeya: “Ai ni hankali na ya fi kwanciya da mai mata ma. Kuma ko za su mutu sai mun shiga.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button