Ba ni da irin kyau da zan iya fitowa takarar Sarauniyar Kyau ta Duniya – Fateema Usman Kinal

“Ba ni da irin kyau da zan iya fitowa takarar Sarauniyar Kyau ta Duniya; mutane ne kawai suke kai ni inda Allah bai kai ni ba. Akwai mutane da suka fi ni kyau, waɗanda ni kaina idan na gansu, suna burge ni.”
– Inji Fatima Kinal (Sarauniyar Arewa)
Tsallewar matashiyar nan, Fatima Usman Kinal, wacce ta samu matsayin “Sarauniyar Arewa” (Queen of the North) a bikin ba da lambobin yabo na Pandora Award da aka gudanar a Jihar Kano, ta bayyana cewa ba ta da irin kyau da za ta iya fitowa takarar Sarauniyar Kyau ta Duniya. Ta yi imanin cewa mutane ne ke ganinta a matsayin mai kyau, amma ita ba ta ganin kanta a wannan matakin ba.
Kamar yadda ta ce: “Ina ji mutane suna cewa ina da kyau, amma ni fa ban taɓa ganin kaina a haka ba. Koɗawar ta yi yawa, ban ji cewa na kai wannan matsayin. Daɗi da ƙari, Alhamdulillah, kowa yana da kyau.”
A cikin wata tattaunawa da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta yi da ita a shirin Podcast, ta kara bayyana cewa: “Ba ni da irin kyau da zan iya fitowa takarar Sarauniyar Kyau ta Duniya. Mutane ne kawai suke kai ni inda Allah bai kai ni ba. Akwai mutane da suka fi ni kyau, waɗanda ni kaina idan na gansu, suna burge ni. Masha Allah.”
Me kuke ganin game da wannan ra’ayi?