Wike Ya Ƙara Ƙaimi Kan Gine-ginen Fasa Kaura a Abuja Bayan Arangama da Sojoji
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai taɓa yarda a ci gaba da yin gine-gine a duk wani fili da aka mallaka ba bisa doka ba a babban birnin Najeriya, Abuja. Wannan furuci nasa ya fito ne bayan wata arangama mai zafi da ya yi da wasu sojojin ruwa ranar Talata a unguwar Gaduwa.
Lamarin ya samo asali ne lokacin da Ministan da tawagarsa suka isa wurin domin duba wani fili da ake zargin an mamaye ba bisa ƙa’ida ba, amma sai wasu dakaru suka hana su shiga.
A cikin bidiyo da hotunan da suka bazu a shafukan sada zumunta, an ga Wike yana tattaunawa cikin tsanani da jagoran rundunar, wanda ya dage cewa ya samu umarni daga maigidansa da kada a bari wani ya shiga wurin.
“Na ba wa jami’an FCTA umarni su tabbatar babu wani gini da za a yi matuƙar ba su da takardun izini ko na mallaka,” in ji Wike ga manema labarai a wurin arangamar.
Ministan ya kuma zargi wasu jami’an tsaro da amfani da mukamansu wajen mallakar filaye ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa hakan na nuna rashin mutunta doka da tsarin gwamnati.
Wike ya yi gargadin cewa gwamnatin tarayya ba za ta ƙara lamuntar da wannan dabi’a ba, musamman ganin yadda wasu ke amfani da sojoji don kare filaye da aka mallaka ta hanyar da bata dace ba.
A cewar wasu masu sharhi a shafukan sada zumunta, wannan arangama ta kara jawo cece-kuce game da batun gine-ginen da ba bisa doka ba a Abuja, inda mutane da dama suka yaba da matakin Ministan, yayin da wasu kuma suka bukaci a gudanar da bincike kan mallakar filayen da ake gardama a kai.













