KannyWood

Baba Sadiq: “Samun Kuɗi Ya Fi Samun Daukaka Wahala a Kannywood”

Ɗaya daga cikin matasan jaruman Kannywood da suka shahara a baya-bayan nan, Baba Sadiq — wanda aka fi sani da Auwal Labarina — ya bayyana cewa samun kuɗi a masana’antar fina-finan Hausa na da matuƙar wahala, fiye da samun daukaka. A cewarsa, akwai lokacin da ya karɓi lambar yabo ta gwarzon jarumi mai tasowa, amma ya dawo gida a ƙafa, saboda babu abin hawa.

“Na karɓi lambar yabo a wani babban taro, amma daga nan sai na dawo gida da ƙafa. Babu motar hawa a lokacin,” in ji shi yayin wata tattaunawa da Hadiza Gabon a shirin Gabon’s Room Talk Show.

Ya Fara Samun Kuɗi Ta Facebook

Baba Sadiƙ ya bayyana cewa yanzu ya fi mai da hankali wajen ɗora abubuwan nishadi da na jarumai mata a shafinsa na Facebook, inda yake samun kuɗaɗe masu yawa ta hanyar tsarin Facebook Monetization.

“Na fahimci mutane ba sa sha’awar bidiyoyin shawarwari, sai na canza salo na fara ɗora bidiyo tare da abokan aikina ‘yan fim. A yanzu haka, ina iya samun fiye da dalar Amurka $300 a kowane lokaci da na ɗora bidiyon da ya jawo hankali,” in ji shi.

Har ila yau, ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗannan bidiyoyin suna kawo masa kuɗi har naira miliyan 5 zuwa 10 a wata, wanda hakan ya sauya masa rayuwa.

See also  Dalilin Da Ya Sa Muka Daina Haska Shirin "Labarina" a Arewa24

Shawara Ga Matasa: Ku Daina Zagin Wasu, Ku Nemi Abin Yi

A ƙarshe, Baba Sadiq ya shawarci matasa su mai da hankali wajen neman hanyar da za ta inganta rayuwarsu, maimakon su ɓata lokaci suna zagin wasu ko yabon mutane da ba su san da su ba.

“Yanzu yawancin matasa sun fi sha’awar magana kan sabuwar motar da Rarara ya siya ko yadda Hadiza Gabon ta yi slimming. Amma da za su nemi abin yi, da sun fi samun ci gaba,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks