Wasanni

Ballon d’Or 2025: Wa zai lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa?

A yau Litinin, 22 ga Satumba 2025, za a karrama gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na duniya ta maza da mata a bikin Ballon d’Or da ake gudanarwa a Theatre du Chatelet, birnin Paris, Faransa.

Ana karrama waɗanda suka fi nuna bajinta a kakar bara, inda aka zaɓi jerin ‘yan wasa 30 da suka cancanci lashe kyautar. Daga cikin jerin, za a bayyana wanda ya fi kwazo a maza da kuma na mata, sannan a jera sauran daga na biyu har zuwa na 30.

BBC ta rairayo manyan ‘yan ƙwallo biyar da ake ganin suna kan gaba a wannan shekarar.

Ousmane Dembele (Paris Saint-Germain)

  • Ya buga wasa 53, minti 3,483
  • Ya zura ƙwallo 35, ya taimaka aka ci 14
  • Ya taimaka wa PSG ta lashe Ligue 1 da Champions League karo na farko a tarihinta
  • Ya zura ƙwallo 21 a Ligue 1, inda ya zama gwarzon gasar
  • A Champions League, ya ci 8, ya taimaka 6
  • Ya ci kwallo a wasannin ƙungiyoyi na duniya da Bayern Munich da Real Madrid
See also  PSG ta Zazzga wa REAL MADRID 4-0

Raphinha (Barcelona)

  • Ya buga wasa 57, minti 4,661
  • Ya zura ƙwallo 34, ya taimaka aka ci 22
  • Ya taimaka wa Barcelona ta lashe La Liga, Copa del Rey, Supercopa de Espana
  • Ya ci 18 a La Liga, inda ya zama gwarzon gasar
  • Ya zura ƙwallo 13 a Champions League, ciki har da uku rigis a Bayern Munich

Harry Kane (Bayern Munich)

  • Ya buga wasa 51, minti 3,955
  • Ya zura ƙwallo 41, ya taimaka aka ci 12
  • Wannan ne kofinsa na farko a tarihin kwallon ƙafa
  • Ya ci ƙwallo 26 a Bundesliga, ciki har da hat-trick sau uku
  • A watan Satumba kawai ya zura ƙwallo 10 a kwana 11, ciki har da huɗu a wasan Dinamo Zagreb
See also  Ronaldo Ya Kafa Tarihi, Portugal Ta Doke Jamus a Gasar UEFA Nations League

Kylian Mbappe (Real Madrid)

  • Ya buga wasa 59, minti 4,742
  • Ya zura ƙwallo 44, ya taimaka aka ci 5
  • Ya ci 31 a La Liga, inda ya zama gwarzon gasar
  • Ya ci hat-trick a ragar Barcelona, sannan ya cire Man City daga Champions League
  • Ya zama ɗan wasa na uku a tarihin Faransa da ya kai ƙwallaye 50

Lamine Yamal (Barcelona)

  • Ya buga wasa 55, minti 4,548
  • Ya zura ƙwallo 18, ya taimaka aka ci 21
  • Ya taimaka Barcelona ta lashe kofuna uku
  • Ya lashe gwarzon ɗan wasa na La Liga a watan Satumba
  • Ya ci ƙwallo biyu a wasan Spain da Faransa a kusa da ƙarshe
See also  Manchester United, Tottenham, Barcelona da Fulham na zawarcin manyan ƴan wasa a kasuwar canja wuri

Duk da cewa jerin sun cika da ‘yan kwallo masu bajinta, kwararru na ganin Mbappe, Dembele da Raphinha ne suka fi yin tasiri a kakar da ta gabata. Sai dai har yanzu ana jiran sakamakon ƙarshe wanda zai nuna wanene ya fi cancanta lashe kyautar Ballon d’Or 2025.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks