KannyWood

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya daga cikin fitattun dattawan masana’antar Kannywood, ya bayyana yadda ya fara harkar wasan kwaikwayo tun a shekarun 1970, kafin daga bisani ya shiga harkar fim a 1994/1995.

A cewarsa, a farkon lokacin yana fitowa ne a matsayin mace, saboda murya tasa tana da laushi wanda ya dace da irin wannan rawa.

Fim ɗinsa na farko shi ne Kilu ta Ja Bau na Hamisu Iyantama, sannan a shekarar 1995 ya fito a fim ɗin So Ne Ko Kauna ƙarƙashin kamfanin Dabo Films — wanda shi ne fim na farko a harshen Hausa da aka nuna a sinima a Kano.

Nakwango ya musanta zargin da ake yi cewa duk ‘yan fim marasa tarbiyya ne, inda ya jaddada cewa “a kowace sana’a akwai nagari da marasa nagarta.”

Ya bayyana cewa ya rage fitowa a fina-finai ne saboda yawancin sabbin fina-finai yanzu ba sa ɗauke da darasin addini ko na al’ada. Ya ce sai dai idan fim ya shafi kira ga Allah ko nuna al’adun Hausawa, to zai shiga.

See also  Ban taba ganin mutuwar da ta girgizani irin ta El-Mu'az ba -Auta Waziri

Fitaccen ɗan wasan ya kuma soki sabon salo na fina-finai, inda ya kira su “fina-finan harshen Hausa” maimakon “fina-finan Hausa na gaske.”

A cewarsa, yawanci suna gauraya Hausa da Turanci, suna kuma ƙunshe da tashin hankali da kwaikwayon rayuwar Turawa — abin da ke lalata ƙimar da tsaftar masana’antar Kannywood.

Duk da haka, Nakwango ya ce bai taɓa nadamar shiga harkar fim ba, domin ta ba shi girmamawa da albarka da ya kejin daɗi a yau.

Ya ƙara da cewa, “na samu taimako a lokuta da dama saboda mutane sun sanni daga cikin fina-finai.”

Ya kuma tuna wani lokaci da aka kama shi bayan ya tsaya wa wani mutum a kotu wanda ya gudu, amma daga bisani aka sake shi saboda shahararsa.

See also  Prenatal care and care for pregnant women is a right for everyone - Ali Nuhu

A cewar Nakwango, ɗansa yana daga cikin manyan editocin fim a Najeriya, kuma ya yi imanin cewa matsayin da Allah ya ba shi cikin masana’antar fim alheri ne daga ƙaddara.

A ƙarshe, ya shawarci abokan aikinsa da su ji tsoron Allah, su kare addini da al’adun Hausawa, su kuma riƙa yafe wa juna.

Haka kuma, ya roƙi al’umma da kada su gaggauta yanke hukunci kan masu fim, domin su ma suna da nagarta da niyyar kawo ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks