KannyWood

Hamisu Breaker da G Fresh A Kotu

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin ɗaurin wata biyar a gidan yari ko biyan tarar naira N200,000 ga shahararrun mawaƙa Hamisu Breaker da G Fresh, bisa kama su da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na Najeriya.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Hamisu Sa’id Yusuf (Breaker) da Abubakar Ibrahim (G Fresh) a gaban kotun. An tuhume su da liƙa da tattaka takardun kuɗi yayin shagulgula da bukukuwa a wurare daban-daban.

A cewar EFCC, kotun ta samu G Fresh da laifin liƙa da tattaka takardun kuɗi na N1,000 har naira N14,000 a cikin shagon Rahama Saidu a watan Nuwamba 2024.

Haka kuma, kotun ta kama Hamisu Breaker da laifin wulaƙanta takardun N200 da suka kai kimanin N30,000 a lokacin wani biki da aka gudanar a garin Hadejia, jihar Jigawa, a cikin watan Nuwamba 2024.

See also  Musa Mai Sana’a Ya Bayyana Ci Gaban Masana’antar Kannywood da Kuma Abubuwan Da Ya Kawo Cikakken Fahimta

Mai shari’a S.M Shuaibu ya bayyana cewa wannan laifi ya saɓa da sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN Act) ta 2007. Daga ƙarshe, ya yanke hukunci ga kowane ɗayan su da ɗaurin wata biyar a gidan yari ko kuma biyan tarar naira 200,000.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks