KannyWood

Da A Ce Ni Ba Dan Fim Ba Ne, Da Na Zama Malamin Addinin Musulunci – Baba Rabe

Shahararren jarumin Kannywood, Abubakar Waziri, wanda aka fi sani da Baba Rabe, ya bayyana wasu muhimman batutuwa dangane da rayuwar jaruman fina-finai da kuma yadda ake kallonsu a cikin al’umma.

A wata hira da ya yi da DW, Baba Rabe ya yi kira ga malaman addini da su shigo cikin masana’antar Kannywood domin yin tasiri mai kyau a cikin fina-finai.

Tarihin Baba Rabe a Fina-Finai da Ilimi

Abubakar Waziri haifaffen Zariya, Jihar Kaduna ne. Ya yi karatu a makarantu daban-daban har zuwa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Zaria), inda ya kammala Diploma a Al’adun Gargajiya.

Baya ga harkar fim, Baba Rabe ma’aikaci ne a Abuja Council for Arts and Culture. A baya kuma, ya yi aiki da Jami’ar Ahmadu Bello a matsayin dan wasan kwaikwayo a sashen Al’adun Gargajiya.

A fagen wakilcin Najeriya, Baba Rabe ya samu damar tafiya kasashe da dama kamar Amurka, China, Afrika Ta Kudu, Korea Ta Arewa, da Korea Ta Kudu, inda ya wakilci ƙasar a bangaren raye-raye da wasan kwaikwayo.

Shin Jaruman Kannywood Masu Ji Da Kai Ne?

Amsar wannan tambaya da aka yi masa, Baba Rabe ya ce:

“Wasu na ganin mu kamar masu girman kai, amma a hakikanin gaskiya, ba haka bane.Muna da rayuwar mu ta yau da kullum, amma saboda kasancewar mu ‘yan fim, mutane da dama na son daukar hotuna da mu ko yi mana tambayoyi.”

Ya kara da cewa wani lokacin hakan na iya jinkirta mu daga yin wasu abubuwan da muka shirya a rayuwa. Amma hakan ba yana nufin muna girman kai ba, sai dai mutane su fahimci yanayin da muke ciki.

Kiran Baba Rabe Ga Malaman Addini

Daga karshe, Baba Rabe ya yi kira ga malaman addini da su daina zagin jaruman fim, a maimakon haka su shigo masana’antar don su taimaka wajen ilmantar da al’umma.

“Da ace ba jarumin fim ba ne ni, to da tabbas zan zama malamin addinin Musulunci, domin ina matukar sha’awar ganin al’umma ta gyaru.”

Ya bukaci a hada karfi da karfe wajen tsaftace masana’antar fim domin amfani da ita a matsayin hanyar ilmantar da al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button