KannyWood

DA NA SANI – Fim ɗin Kannywood da Ya Dace Ka Kalla!

Na dade ban kalli fim ɗin Kannywood da ya burge ni sosai ba — sai da na ci karo da fim ɗin “Da Na Sani.” Wannan ba jerin shirye-shirye ba ne (series), fim ɗaya ne tilo, amma cike da darussa, nishadi da kuma fadakarwa.

Me Ya Sa “Da Na Sani” Ya Bambanta?

Fim ɗin ya yi fice wajen nuna illar yadda wasu maza ke kasa rage girman kai domin su gudanar da rayuwar aure da matan da suka aura — musamman idan matan sun fi su nisan shekaru. An gabatar da sakon da ya taba zuciya cikin salo mai sauƙi kuma daidai da al’ada.

Godiya Ga Masu Ruwa da Tsaki

Dole ne a yaba wa:

  • Amina Adam – mai shirya fim
  • Bifa Mohammed – darakta
  • Jaruman fim ɗin – musamman Momo, Samira, da Tahir I. Tahir waɗanda suka nuna bajinta.

Momo Da Zallar Acting

Ina nan dai da maganata: Idan kana son ganin zallar wasan kwaikwayo a Kannywood — ka nemi Momo ko Sadiq Sani Sadiq. Za ka manta kana kallon fim, ka ji kamar gaskiya ne!

Fim ɗaya, Gida ɗaya, Ma’ana mai zurfi

Abin burgewa shi ne yadda aka kammala fim ɗin a gida ɗaya, da ‘yan jarumai kaɗan, amma ya ɗauki zuciya saboda zurfin saƙonsa da kuma yadda aka tsara shi cikin natsuwa.

Sabon Tsari Daga Taskar Kannywood

Taskar Kannywood na shirin kawo sabon tsari: kallon fim guda ɗaya a kowane mako. Idan wannan ya tabbata, zai rage dogon kallon jerin shirye-shirye, a koma kallon cikakkun fina-finai masu inganci.

Daga: Mutawakkil Gambo

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button