KannyWood

ALI NUHU YA GARGADI RAYYA KWANA CASA’IN KAN SHIRIN ZANA TATTOO

JARUMA Rayya ta yi tambaya kan yadda mutane za su ji idan ta zana Tattoo, lamarin da ya jawo ‘yan Kannywood da dama suka yi martani. Shugaban hukumar fina-finan Najeriya, Ali Nuhu, ya gargade ta da cewa:
“Ke! Kar ki soma wallahi. Bulalar nan tana nan ban jefar da ita ba.”

Tambayar Rayya a shafinta na Instagram ta jawo cece-ku-ce daga abokan sana’a da masoyanta, ciki har da waɗannan martanin:

Madam korede: “Wallahi za ki kara kyau Rayyah dan kaniyanki.”

Officialzeezango_: “Kar ki yi gaskiya.”

Nasirualikoki1: “Ki rufa mana asiri.”

nazir_danhajiya: “Zan zane ki har sai kin yi kuka.”

Wasu daga cikin shugabannin masana’antar Kannywood da masoya sun nuna rashin amincewarsu kan wannan yunkuri, suna mai cewa bai dace ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button