Daga Cikon Benci Zuwa Cikakken Jarumin Kannywood – Abubakar Waziri

ABUBAKAR WAZIRI: JARUMIN DA YAKE FITOWA A MATSAYIN MARA TAUSAYI A KANNYWOOD
A ‘yan shekarun nan, idan aka tambayi masu sha’awar kallon fina-finan Hausa cewa, wane jarumi ne ya fi dacewa da fitowa a matsayin mara tausayi a masana’antar Kannywood, mafi yawan amsoshin za su kasance Abubakar Waziri ko Baban Ma’u.
Tarihin Abubakar Waziri
Asalin sunansa Garba Muhammad, an haife shi a Samaru, Zariya, Jihar Kaduna. A halin yanzu, ya na zaune a Abuja, babban birnin tarayya.
Waziri ya bayyana cewa, shigarsa harkar fim ta kasance bazata, domin yana zaune a Abuja lokacin da masu shirya fina-finai suka zo daukar wani shiri. Sai suka bukaci ya fito a matsayin ɗan cikon benci. Daga nan ne aka fahimci baiwar da ke tattare da shi, wanda hakan ya sa aka ci gaba da ba shi manyan ayyuka.
Fina-Finan Da Ya Fito A Ciki
Zuwa yanzu, Abubakar Waziri ya fito a cikin manyan fina-finan da suka samu karbuwa sosai a masana’antar Kannywood. Wasu daga cikin fina-finan da ya taka rawa a ciki sun hada da:
- Allah Ya Hana Babu
- Kisan Gilla
- Labarina
- Garwashi
- Manyan Mata
A mafi yawancin fina-finai, Waziri na fitowa a matsayin mugun mutum ko mara imani, wanda hakan ya kara masa shahara a masana’antar.
Shin A Zahiri Ma Mugu Ne?
Dangane da yadda mutane ke daukarsa a matsayin mugu a zahiri, Waziri ya bayyana cewa hakan ba gaskiya ba ne. A cewarsa:
“Akwai wani mutum da na taɓa haɗuwa da shi sai ya ce min, ‘Allah ya tsine maka albarka.’ Sai na ce da shi, malam, wannan magana taka ta yi tsauri sosai. Domin kuwa yadda nake a fim ba haka nake a zahiri ba.”
Haka kuma, ya bayyana cewa har yara nasa sun taɓa dawowa daga makaranta suna cewa ana ce musu ‘ya’yan mugu.’ Sai ya ce musu su yi hakuri kada su damu da maganganun mutane.
Abubakar Waziri ya zama daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, musamman wajen fitowa a matsayin mugu. Duk da haka, ya tabbatar da cewa hakan bai shafi halayyarsa a zahiri ba. A cewarsa, fim wani aiki ne da dole mai yinsa ya yi kokari wajen ba da gudunmawa yadda ya kamata.