Dalilin Da Ya Sa Aka Daina Saka Ni a Fim – Baballe Hayatu

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Baballe Hayatu, ya bayyana dalilin da ya sa aka daina saka shi a cikin fina-finan Kannywood na wasu shekaru baya. A cewarsa, hakan ya kasance wani babban kalubale a rayuwarsa da ba zai taɓa mantawa da shi ba.
Baballe ya bayyana wannan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin “Mabiya Shafina” na Fact News Hausa. A cikin hirar, ya bayyana cewa wasu matsaloli na cikin gida a masana’antar Kannywood ne suka haddasa hakan, ciki har da son zuciya da rashin adalci daga wasu daga cikin masu ruwa da tsaki.
Jarumin ya kara da cewa duk da wannan jarrabawa, bai taba daina fatan alheri ga masana’antar ba, kuma ya ci gaba da kasancewa da kyakkyawar zuciya ga abokan aikinsa. A cewarsa, wannan lokaci ne da ya koya masa darussa da dama a rayuwa.
Ga masu son kallon cikakken bidiyon hirar, za su iya ziyartar shafinmu na YouTube a Fact News Hausa domin kallon shirin “Mabiya Shafina” da ya gabata.