KannyWood

Dalilin Da Ya Sa Muka Daina Haska Shirin “Labarina” a Arewa24

Masoya sun yi ta tambaya: “Me ya sa ba a sake nuna Labarina a Arewa24 ba?” Ga bayani a sauƙaƙe.

1. Kasuwancin Mu Ya Canza

Misali, idan kuna biyan kuɗi don sayen ruwa daga wani, kuma kun sami firiji naku, shin za ku ci gaba da biyan kuɗin ruwan? A’a.

Haka ne muka yi. Tinda gamu da tashar mu ba ma buƙatar biyan Arewa24 domin haska shirin.

2. Ku Ne Sukayi Shirin Popular

Alhamdulillah, ku ne sukasa Labarina tare da goyon bayanku. Don haka, muna son ku sami shi cikin sauƙi:

  • Da farko (Season 1 & 2): Arewa24 kawai tana watsawa.
  • Yanzu: Kuna iya kallon shirin kyauta a:
    YouTube (don duba sake)
    Saira Movies TV (a satellite— Eutesalat/Nilesat/Amos 17)

3. Ba Adawa Ba, Amma Tattalin Arziki

Ba mu yi wa Arewa24 rigima ba. Kullum muna biyan su don watsa shirin. Yanzu muna da tashar mu, don haka muka daina biyan kuɗin.

Inda Za’a iya Kallon Labarina Yanzu

🔍 Nemi Saira Movies TV akan:

  • Nilesat
  • Eutelsat
  • Amos 17

Wannan canjin ya taimaka mana mu ƙara haɓaka. Na gode da ƙaunarku!

Ahmad Nagudu
Media Promoter, Saira Movies Investment Ltd.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button