Dan Small Ya Karyata Ikirarin Soja Boy Kan Biyan Kudi a Kannywood

FITACCEN FURODUSA ABDULAZIZ DAN SMALL YA KARYATA IKIRARIN SOJA BOY KAN CEWA BABU WANDA YA TABA BIYANSA A MASANA’ANTAR KANNYWOOD
Fitaccen furodusa a masana’antar Kannywood, Abdulaziz Dan Small, ya karyata ikirarin jarumin Soja Boy kan cewa babu wanda ya taba biyansa kudi a masana’antar.
Dan Small ya bayyana cewa ya taba bawa Soja Boy kudi har sau biyu, kuma ya kara masa kudi a matsayin taimako cikin mutunci da kyautatawa. A cikin wata bidiyo da aka wallafa, furodusan ya ce yana da hujjoji kan batun, har ma ya ce ya taba biya wa Soja Boy kudin hotel har N200,000 da kuma N100,000.
ASALIN MAGANAR SOJA BOY
Soja Boy ya yi ikirarin cewa ya yi fina-finai da dama a masana’antar Kannywood amma ya ce taimako kawai ya ke yi ba tare da an taba biyansa ba. Wannan ya fito ne bayan dakatar da shi daga masana’antar, inda ya yi bugun kirji cewa shi ba ya dogara da Kannywood.
MARTANIN DAN SMALL
Dan Small ya bayyana cewa maganganun Soja Boy sun bashi mamaki da takaici saboda alakar mutunci da suka taba yi a baya. Ya ce:
“Farkon zuwansa, ya min kwana hudu, na dauki N200,000 na bayar a matsayin kudin hotel. A karo na biyu kuma, ya sake dawowa, na ba shi N100,000. Ranar da zai tafi, na kara daukar N50,000 na bashi na ce Soja Boy ka kara mai.”
Furodusan ya ce Soja Boy ya bayyana cikin fina-finai kamar Barauniyar Amarya, wanda ya tabbatar ya taba biyansa kudi a cikinsa.
TAKAICI DA KALUBALE
Dan Small ya kalubalanci Soja Boy kan alfaharin da yake yi, tare da cewa bai kamata ya yi irin wannan ikirari ba bayan duk taimakon da aka masa. Ya ce yana da cikakken tabbaci kan abin da ya fadi, kuma yana jiran duk wanda zai karyata shi.
Wannan martani ya ja hankalin mutane da dama a shafukan sada zumunta, musamman a tsakanin masoya fina-finan Kannywood.