Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soja kan Najeriya, yana zargin gwamnatin ƙasar da yin shiru yayin da ake kashe mabiya addinin Kirista.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka “na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don murƙushe ƴan ta’adda masu tsaurin kishin Islama” da ke aikata ta’asa a ƙasar.
Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimako da gwamnatin Amurka ke bai wa Najeriya, yana mai cewa “ba za mu ci gaba da taimaka wa ƙasar da ke wulakanta Kiristoci ba.”
Najeriya ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa babu wani shirin kisan gilla da ake yi wa Kiristoci a yankin arewaci, inda galibi Musulmai ke zaune.
A sakonsa na ranar Asabar, Trump ya ce ya ba ma’aikatar tsaron Amurka umarni ta fara shirin ɗaukar mataki kan Najeriya “idan har gwamnatin ƙasar ta kasa dakatar da kisan Kiristoci.”
Trump wanda ke da’awar samun lambar yabo ta zaman lafiya, ya kuma yi kalamai masu tsauri ga Najeriya, inda ya ce “Amurka za ta shiga cikin ƙasar da a yanzu ta wulakanta.”
Tun a ranar Juma’a Trump ya wallafa cewa ana kashe dubban Kiristoci a Najeriya, kuma masu tsattsauran ra’ayin Islama ne ke aikata hakan — duk da cewa bai gabatar da wani hujja ba.
Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka ne suka fara yada wannan zargi tun a watan Maris, lokacin da ɗan majalisar Chris Smith ya kira a saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa a kansu.
Haka kuma a watan Oktoba, Sanata Ted Cruz da ɗan majalisar Riley Moore — dukkansu ‘yan jam’iyyar Republican — suka zargi gwamnatin Najeriya da rashin ɗaukar mataki game da kisan Kiristoci.
Wadannan kalamai sun ƙara wa masu da’awar ana kashe Kiristoci ƙwarin gwiwa a Najeriya, ƙasar da ta shafe shekaru tana fama da rikicin ƙabilanci da na addini.
Najeriya dai na fama da tashin hankali da dama, inda masana ke cewa ana kashe Musulmai da Kiristoci ba tare da bambanci ba, musamman a yankunan arewa maso gabas da arewa maso tsakiya.
🏛️ Martanin Gwamnatin Najeriya
Babu wani sabon martani kai tsaye daga gwamnati bayan barazanar da Trump ya yi, amma Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani a shafinsa na X cewa ikirarin ba shi da tushe.
“Yancin gudanar da addini shi ne ginshiƙin Najeriya, kuma hakan zai ci gaba da kasancewa,” in ji Tinubu.
Haka ma ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar da sanarwa tana musanta ikirarin Trump. “Ƴan Najeriya suna da cikakken ‘yanci wajen gudanar da addininsu, kuma babu wani bangare da ake tauye masa ‘yanci,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta ce a karkashin shugabanci Tinubu, ana ƙoƙari sosai wajen yaki da ta’addanci da kare rayukan al’umma ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila ba.
Ta kara da cewa Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da sauran ƙasashen duniya don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
⚖️ Matsalolin Tsaro Da Ke Ƙasar
Najeriya ƙasa ce da ke da yawan Musulmai a arewaci da kuma Kiristoci a kudanci. Duk da haka, tana ci gaba da fama da matsalolin tsaro masu tarin yawa.
A yankin arewa maso gabas, kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane tare da raba sama da mutum miliyan biyu da muhallansu.
A arewa maso yamma kuma, ƴan fashin daji na ci gaba da kai hare-hare da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
A yankin tsakiyar ƙasar kuma, rikicin makiyaya da manoma ya zama babban kalubale, wanda galibi ake danganta shi da bambancin addini tsakanin manoma Kiristoci da makiyaya Musulmai.
Ko a wa’adinsa na farko, Trump ya taɓa saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa da su, kafin shugaban Amurka Joe Biden ya cire sunan ƙasar daga jerin a shekarar 2021.













