KannyWood

Falalu A. Dorayi: Lokaci Ya Yi da Kannywood Za Ta Dawo Gidajen Gala

Daya daga cikin fitattun daraktoci kuma jarumai a Kannywood, Falalu A. Dorayi, ya yi kira ga masana’antar da ta sake duba hanyoyin samun kudade a fina-finai.

A wata hira da RFI Hausa, Dorayi ya bayyana cewa sauye-sauyen zamani sun shafi yadda ake kallon fina-finai. A cewarsa, “Yanzu kida ya canza, to rawa ma ta canza,” yana nufin cewa dabarun kasuwancin fina-finai na bukatar sabuntawa.

Gidajen Gala Su Na Samun Nasara

Dorayi ya ce akwai sauyi matuƙa a harkar samun kudade. A baya, gidajen Gala na taka rawa sosai wajen tallata fina-finai. Yanzu haka, inda ba don tashoshin YouTube ba, da masana’antar ta Kannywood na iya fuskantar babbar matsala wajen samun kuɗi.

“Ina ganin akwai buƙatar mu koma ga gidajen Gala. Na san fina-finai da suka samu fiye da naira miliyan daya a rana guda a wadannan wurare,” in ji Dorayi.

Kalubale A Hanyar Intanet

A cewarsa, akwai daruruwan masu downloading a Arewacin Najeriya, amma kuɗin da ake samu bai taka kara ya karya ba — tsakanin naira miliyan daya zuwa biyu. Haka kuma, yawancin masu kallo ba sa iya kashe data don kallon fim a YouTube ko shafukan intanet.

Taimako Daga Masu Ruwa da Tsaki

Dorayi ya yi nuni da cewa har yanzu akwai masu sha’awar kallon fina-finai a gidajen Gala daga karfe 5 na yamma har zuwa 12 na dare. Ya ce idan aka ci gaba da haskawa a irin waɗannan wurare, masana’antar za ta sami sabbin hanyoyin samun riba.

Kira Ga Hadin Kai

A ƙarshe, ya bukaci hadin kai daga gwamnati, masu zuba jari, da sauran masu ruwa da tsaki don dawo da martabar masana’antar. Ya ce hakan zai taimaka wajen ceto fina-finan Hausa daga durkushewa.

  • Kannywood
  • Falalu A. Dorayi
  • Gidajen Gala
  • Fina-finan Hausa
  • Hanyoyin samun kudi a Kannywood
  • Sabbin dabarun tallata fim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button