Sansanin Super Eagles na Najeriya ya bude aiki a hukumance ranar Lahadi a birnin Rabat, kasar Maroko, bayan zuwan ‘yan wasa goma domin fara shirin karshe na gasar cin tikitin zuwa FIFA World Cup 2026 (CAF Playoffs).
Rukunin farko na ‘yan wasa da jami’an kungiyar sun isa Hotel Rive da ke Rabat da yammacin Lahadi, wanda ya nuna farkon mako mai matukar muhimmanci ga Najeriya a yunkurinta na komawa babban matakin kwallon kafa na duniya.
Mai magana da yawun kungiyar, Promise Efoghe, ya bayyana wa Hukumar Labarai ta Najeriya (NAN) cewa wadanda suka fara isa sun hada da Calvin Bassey, Alex Iwobi, Samuel Chukwueze, tare da Tolu Arokodare da Olakunle Olusegun.
“Daga baya a ranar Lahadi, ‘yan wasa uku — Wilfred Ndidi, Moses Simon, da William Troost-Ekong — sun iso sansanin, wanda hakan ya kai adadin ‘yan wasa takwas.
Da daddare kuma, Benjamin Fredericks da Chidozie Awaziem sun iso, wanda ya kara yawan ‘yan wasan sansani zuwa goma yayin da shirin ya kara zafi,” in ji shi.
A ranar Asabar da ta gabata, koci Eric Chelle ya kammala zabar jerin ‘yan wasa 24 da za su fafata a wasan share fagen karshe, inda ya hada ‘yan wasa daga Turai da kuma na cikin gida don karawa a Rabat.
Wasan Farko Da Jadawalin Gasar
Super Eagles za su fafata da Gabon a wasan farko ranar Alhamis. Nasara a wannan wasa za ta kai su wasan karshe na nahiyar Afirka da Kamaru ko Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ranar 16 ga Nuwamba, shima a Rabat.
Wannan zagaye na playoff na CAF yana ba kungiyoyin Afirka damar karin hanya zuwa gasar duniya ta FIFA 2026. Duk da haka, duk mai lashe wannan jerin wasanni zai sake buga wasa da wakilai daga wasu nahiyoyi a Maris 2026 a kasar Mexico domin karshe tabbatar da shiga gasar.
Sauye-Sauye A Tawagar
Kocin Chelle ya yi wasu canje-canje a tawagar da ta buga wasannin cancanta na watan da ya gabata, inda Najeriya ta doke Lesotho da Benin, wanda hakan ya kai ta matsayi na biyu a bayan Afirka ta Kudu. Wadannan nasarori ne suka ba Super Eagles damar shiga zagayen playoff a matsayin daya daga cikin kungiyoyi hudu mafiya kyau a rukunin Afirka.
Daga cikin wadanda suka dawo akwai Maduka Okoye na Udinese, wanda zai kara gogayya a bangaren tsaron raga, da kuma Chidozie Awaziem a bangaren baya.
Haka kuma an dawo da Raphael Onyedika da Chidera Ejuke domin kara kuzari a tsakiya da gaba.
Wasu ‘yan wasa da ba su samu gurbi ba a wannan karo sun hada da Felix Agu, Terem Moffi, da Christantus Uche.
Kocin Chelle ya jaddada cewa, ko da yake Najeriya ce tafi daraja a cikin tawagogi hudu da ke wannan zagaye, bai kamata su yi sakaci ba. Ya yi kira da a kara natsuwa, tsari, da bin dabaru domin cimma nasara.
Jerin Sunayen Tawagar Najeriya Don Wasan Playoffs Na FIFA World Cup 2026
Masu Tsaron Raga:
- Stanley Nwabali (Chippa United, Afirka ta Kudu)
- Amas Obasogie (Singida Blackstars, Tanzaniya)
- Maduka Okoye (Udinese, Italiya)
’Yan Baya:
- Chidozie Awaziem (Nantes, Faransa)
- Semi Ajayi (Hull City, Ingila)
- Calvin Bassey (Fulham, Ingila)
- Benjamin Fredericks (Dender, Belgium)
- Bruno Onyemaechi (Olympiakos, Girka)
- Bright Osayi-Samuel (Birmingham City, Ingila)
- Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal)
- William Troost-Ekong (Al-Kholood, Saudiyya)
’Yan Tsakiya:
- Alex Iwobi (Fulham, Ingila)
- Wilfred Ndidi (Besiktas, Turkiyya)
- Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium)
- Frank Onyeka (Brentford, Ingila)
- Alhassan Yusuf (New England Revolution, Amurka)
’Yan Gaba:
- Akor Adams (Sevilla, Sifaniya)
- Tolu Arokodare (Wolverhampton Wanderers, Ingila)
- Samuel Chukwueze (Fulham, Ingila)
- Chidera Ejuke (Sevilla, Sifaniya)
- Ademola Lookman (Atalanta, Italiya)
- Olakunle Olusegun (Nizhny Novgorod, Rasha)
- Victor Osimhen (Galatasaray, Turkiyya)
- Moses Simon (Paris FC, Faransa)













