KannyWood

Fitattun Jaruman Kannywood: Wadanda Suka Tabbatar da Matsayinsu a Masana’anta

Masana’antar fina-finan Hausa, wato Kannywood, ta daɗe tana haifar da taurari masu haske a fagen shirya da fitowa a fina-finai. Wasu sun shahara, suka bar tarihi, yayin da wasu suka shigo su yi ɗan ɗanɗano su ɓace. Amma a cikin wannan rikici da sauyin zamani, akwai jarumai da suka daɗe suna tsayawa da kafafunsu, suna cigaba da jan zarensu a idon duniya.

Wasu daga cikinsu sun fara tun daga shekaru na baya, har yanzu suna cikin sabbin shirye-shirye da ke jan hankali a kafafen watsa labarai da talabijin. Ga jerin wasu daga cikin su:

Ali Nuhu

Ali Nuhu ya shafe fiye da shekaru ashirin yana taka muhimmiyar rawa a finafinan Hausa. Yanzu haka shi ne shugaban Hukumar Fim ta Najeriya, kuma ana yi masa lakabi da “Sarkin Kannywood.” Fim ɗinsa na farko, Abin Sirri Ne, ya fito a shekarar 1999. Daga lokacin ne har yanzu bai sauka daga kololuwa ba.

Yakubu Mohammed – Mawaki, Marubuci, Jarumi

Yakubu Mohammed ya fara ne a matsayin mawaki da marubuci a ƙarshen shekarun 90, kafin daga bisani ya fara fitowa a fim. Tun daga lokacin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman da ke da cikakken hazaka da tsari a fagen wasan kwaikwayo.

Hajara Usman – Mama Hajjo

Hajara Usman, wadda aka fi sani da Mama Hajjo, ta fi shekaru 36 a harkar fim. Ta fara ne da finafinai kamar Farin Wata da Bakar Gizo. A yau, tana daga cikin manyan mata da ke fitowa a finafinai kamar Manyan Mata, inda take ci gaba da burge masu kallo.

Rabiu Rikadawa – Baba Dan Audu

Rabiu Rikadawa ya fi fice a matsayin jarumin finafinan talabijin. Ya fara shahara da sunan “Dila”, amma yanzu ana jin sunansa da rawar da yake takawa a matsayin Baba Dan Audu, musamman a shirye-shiryen Labarina da Gidan Sarauta.

Sadiq Sani Sadiq

Shi ma yana daga cikin waɗanda suka shigo fim tun yana ƙarami, karkashin jagorancin Ali Nuhu da Sani Danja. Har yau yana daga cikin jaruman da ke jan hankali a fina-finai, yana haskakawa da ƙwarewa.

Jamila Nagudu

Jamila Nagudu ta fara ne tun 2002. Tana daga cikin fitattun jaruman mata da ke da soyayya a zukatan jama’a. Finafinanta na baya sun hada da Jamila da Jamilu, Ƙauyawa, da Hindu. A yanzu haka tana taka rawa a finafinai irin su Manyan Mata.

Lawal Ahmad

Lawal Ahmad ya kasance jarumi tun zamani irin na Taraliya, Sansani, da Sai Wata Rana. Sai dai daga baya ya ɗan ja baya, kafin ya dawo da sabon karfi a fim ɗin Izzar So, inda ya ƙara bayyana bajintarsa.

Tijjani Faraga

Tijjani Faraga ya fara fim ne tun daga Jos, a cikin finafinan daɓe. Yana daga cikin tsofaffin jaruman da har yanzu ake jin tasirinsu a masana’antar.

Sauran Jarumai Masu Tasiri

Baya ga su, akwai wasu da suka daɗe ana kallon su kamar:

  • Bashir Nayaya
  • Tahir Fagge
  • Musa Muhammad (Auta Baita)
  • Shuaibu Lilisco

Duk da wasu daga cikinsu ba a cika ganin su kai tsaye ba, amma har yanzu suna nan da darajarsu a zukatan masu kallon fina-finan Hausa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button