Ganduje Ya Sauka Daga Shugabancin Jam’iyyar APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sauka daga mukaminsa a matsayin shugaban jam’iyyar nan take a ranar Juma’a.
Majiyoyi daga uwar jam’iyyar APC a Abuja da wasu da ke kusa da tsohon shugaban jam’iyyar sun tabbatar wa da TRT Afrika Hausa labarin saukar, duk da cewa babu wata sanarwa ta hukuma da aka fitar a hukumance a lokacin da rahoton nan ke fitowa.
Dalilin Saukar?
Har yanzu ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa Ganduje ya sauka daga kujerar ba. Sai dai wasu majiyoyi sun ce hakan na da nasaba da matsalolin lafiya da yake fuskanta.
Wanene Zai Gaje Shi?
A halin yanzu, babu wanda aka tabbatar zai maye gurbin Ganduje a matsayin sabon shugaban jam’iyyar. Amma tun tuni wasu ‘yan jam’iyyar daga yankin Arewa ta Tsakiya ke neman a maido da shugabancin jam’iyyar zuwa yankin, kasancewar tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu, daga yankin ya fito.
Tarihin Naɗin Ganduje
A watan Agusta 2023, ne aka naɗa Ganduje — tsohon gwamnan jihar Kano — a matsayin shugaban rikon kwarya na APC. Wannan naɗin ya biyo bayan murabus da Sanata Abdullahi Adamu ya yi, watanni kaɗan bayan rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.
Ganduje ya kasance daya daga cikin fitattun magoya bayan Tinubu, tun kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar da ya ba shi tikitin takara.