Goodluck Jonathan 2027: Muhawara kan kundin tsarin mulkin Najeriya

Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 a Najeriya, wata sabuwar muhawara ta ɓarke kan halascin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya sake tsayawa takara.
A ƙarƙashin dokokin Najeriya, mutum ba ya wuce sau biyu a zaɓe a matsayin shugaban ƙasa. Wannan ya sanya wasu na ganin Jonathan ba shi da hurumin tsayawa takara, domin ya sha rantsuwar kama aiki sau biyu. Sai dai magoya bayansa na cewa abin da kundin tsarin mulkin ya tanada shi ne zaɓe sau biyu, ba wai rantsuwa ba.
Wannan batu ya janyo zazzafar muhawara tsakanin ƴan siyasa da masana shari’a, inda aka rarrabu kan fassarar sashe na 137 (III) na kundin tsarin mulkin da aka yi masa gyara a 2017.
Mulkin da Jonathan ya yi a baya

Goodluck Jonathan ya fara zama shugaban ƙasa a 2010 bayan rasuwar Umaru Musa Ƴar’adua. Ya yi saura wa’adin shekaru biyu da suka rage, kafin ya tsaya takara a 2011, inda ya yi nasara.
Bayan haka aka sake rantsar da shi karo na biyu, inda ya yi wa’adin shekara huɗu (2011 zuwa 2015). Jimillar shekarun mulkinsa ya kai shida.
Me doka ta ce?
Barista Abba Hikima Fagge, lauya kuma masanin kundin tsarin mulki, ya ce kundin tsarin mulkin ya fayyace cewa duk wanda ya yi wa’adin mulki biyu ba ya da ikon sake tsayawa takara.
Ya ce idan aka rantsar da mataimakin shugaban ƙasa domin ya ƙarasa wa’adin wanda ya mutu ko aka tsige shi, wannan za a ƙirga shi a matsayin wa’adi guda, koda kuwa bai cika shekara huɗu ba.
Shin Jonathan na da damar sake tsayawa takara?
Barista Hikima ya ce gyaran kundin tsarin mulkin da aka yi a 2017 ba ya waiwaye baya, saboda haka ba ya shafar Jonathan da mulkinsa da ya ƙare tun 2015.
A cewarsa, idan aka yi amfani da ƙa’idar doka ba ta waiwaye, to tsohon shugaban ƙasar na iya tsayawa takara. Har ma ya ambaci cewa kotu ta taɓa tabbatar da cewa Jonathan na da damar tsayawa takara, duk da cewa daga baya kotun ɗaukaka ƙara ta kori ƙarar bisa dalilan fasaha na shari’a.
Matsayin Kotun Ƙoli

Duk da haka, lauyan ya bayyana cewa kotun ƙoli ce kaɗai za ta iya yanke hukunci na ƙarshe kan wannan muhawara.
“Idan ana son samun cikakken bayani, dole ne a je kotun ƙoli domin ita ce za ta fayyace wannan dambarwa,” in ji shi.
Jonathan bai bayyana aniyarsa ba
Har yanzu dai Goodluck Jonathan bai fito fili ya ce zai tsaya takara a 2027 ba. Sai dai rahotanni daga makusantansa na cewa yana tattaunawa da abokan shawararsa.
Idan ya tsaya takara kuma ya samu damar yin nasara, zai zama mutum na farko a tarihin Najeriya da ya taba rike shugabancin ƙasa sannan ya dawo takara bayan tsawon shekaru da saukarsa daga mulki.