• Latest
  • Trending
  • All
Hoton jami’an tsaro suna tsaye a wani gari na Jihar Katsina yayin wani taron sulhu da yan bindiga da suka tuba.

Gwamnatin Katsina Ta Ce Tallafin Da Ta Baiwa Yan Bindiga Da Suka Tuba Zai Rage Matsalar Tsaro

September 16, 2025
Najeriya 4–1 Gabon: Super Eagles Sun Tsallake Zuwa Wasan Karshe

Najeriya 4–1 Gabon: Super Eagles Sun Tsallake Zuwa Wasan Karshe

November 13, 2025
Ba zan bari a gina filin da ba shi da takardu ba – Ministan Abuja Wike

Ba zan bari a gina filin da ba shi da takardu ba – Ministan Abuja Wike

November 12, 2025
Matsalar Tsaro a Kano: 'Yan sa kai na ƙauyen Shanono suna sintiri domin kare al’umma daga harin ƴan bindiga.

Matsalar Tsaro a Kano: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Faruruwa, Sun Yi Garkuwa da Mata Biyar

November 12, 2025
NYSC Ta Fitar da Lambobin Kira Ga Mambobin Batch C Na 2025

NYSC Ta Fitar da Lambobin Kira Ga Mambobin Batch C Na 2025

November 11, 2025
Rikicin Nyesom Wike da Sojojin Najeriya: Abin da ya faru a Abuja

Rikicin Nyesom Wike da Sojojin Najeriya: Abin da ya faru a Abuja

November 11, 2025
Tsohon Gwamnan Rivers Nyesom Wike tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Alkali James Omotosho yayin rikicin siyasa na dokar ta-baci a Jihar Rivers, Najeriya, 2025.

Rikicin Siyasar Jihar Rivers: Wike, Tinubu, da Alkali James Omotosho

November 11, 2025
Dharmendra Ya Kwantar da Hankalin Masoyansa Bayan Shiga Asibiti

Dharmendra Ya Kwantar da Hankalin Masoyansa Bayan Shiga Asibiti

November 10, 2025
Farkon Shirin Super Eagles Don Wasan Takarar Karshe Na Fifa World Cup 2026 a Rabat

Farkon Shirin Super Eagles Don Wasan Takarar Karshe Na Fifa World Cup 2026 a Rabat

November 10, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar da Tsaro Duk da Gargadin Tafiye-Tafiye Daga Gwamnatin Birtaniya

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar da Tsaro Duk da Gargadin Tafiye-Tafiye Daga Gwamnatin Birtaniya

November 10, 2025
Majalisar Dattawa Ta Musanta Zargin Karbar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Majalisar Dattawa Ta Musanta Zargin Karbar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga ₦877 zuwa ₦828 kowace lita, raguwar kashi 5.6%. Masana sun ce hakan zai taimaka rage tashin farashi.

Kamfanin Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦828 Kowace Lita

November 8, 2025
Naira Ta Kara Dorewa: Dala Ta Karkata Tsakanin ₦1,437 Zuwa ₦1,455 a Kasuwar Musayar Kudi

Naira Ta Kara Dorewa: Dala Ta Karkata Tsakanin ₦1,437 Zuwa ₦1,455 a Kasuwar Musayar Kudi

November 7, 2025
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
Friday, November 14, 2025
NgHausa News
  • Login
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
No Result
View All Result
NgHausa News
No Result
View All Result
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
🚀 Join Our Telegram Community
Home Nigeria

Gwamnatin Katsina Ta Ce Tallafin Da Ta Baiwa Yan Bindiga Da Suka Tuba Zai Rage Matsalar Tsaro

by NgHausa
September 16, 2025
0
Hoton jami’an tsaro suna tsaye a wani gari na Jihar Katsina yayin wani taron sulhu da yan bindiga da suka tuba.

RUETERS

0
SHARES
12
VIEWS

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa matakin tallafawa Yan bindiga da suka tuba ya samo asali ne daga bukatar magance manyan dalilan da suka jefa su cikin aikata laifi, musamman rashin ilimi da rashin aikin yi.

A cewar gwamnati, waɗannan dalilai ne suka taka muhimmiyar rawa wajen haifar da matsalar tsaro da jihar ke fama da ita.

Kwamishinan tsaro na jihar, Dokta Nasiru Matazu, ya bayyana cewa Yan bindiga da suka tuba suka mika wuya sun roki gwamnati ta samar musu da makarantu domin ƙara ilimantar da yaransu, asibitoci don kula da lafiyarsu, da kuma wuraren shan ruwa ga shanunsu.

Ya ce samar da waɗannan abubuwa zai taimaka wajen tabbatar da cewa masu laifin da suka tuba ba za su koma ga munanan ayyukan baya ba.

See also  Rikicin Siyasar Jihar Rivers: Wike, Tinubu, da Alkali James Omotosho

Sai dai masana harkokin tsaro sun yi jan hankali, suna cewa bai kamata a mayar da hankali ga tallafawa ƴan bindiga kawai ba.

Dokta Kabiru Adamu, ƙwararre a fannin tsaro, ya bayyana cewa ya kamata a fi karkatar da irin wannan tallafi zuwa ga al’ummomin da matsalar ta shafa kai tsaye.

A cewarsa, akwai al’ummomin da suka rasa shanu, dukiyoyi, da ‘yan uwa sakamakon hare-haren ƴan bindiga, don haka su ne suka fi bukatar tallafin gwamnati.

Ya kuma yi gargadi cewa rarraba tallafi kai tsaye ga ƴan bindiga na iya ƙara musu ƙwarin guiwa, har ma ya zama kamar an ba su lada saboda aikata laifi.

See also  TIN a Najeriya: Yadda Ake Samunta, Muhimmanci da Tasirin Dokar Haraji 2026

“Ba duka yan bindigan suka shiga ne saboda ƙuncin rayuwa ba. A cikinsu akwai waɗanda suka mayar da sata da garkuwa da mutane sana’a,” in ji shi.

Matakin gwamnatin Katsina na zuwa ne bayan wasu al’ummomin jihar sun shiga tattaunawar sulhu da yan bindiga.

Duk da haka, rahotanni sun nuna cewa sulhun bai dakatar da hare-haren yan bindiga a wasu jihohin da ke makwabtaka da Katsina ba, inda har yanzu ake fuskantar matsaloli na tsaro.

Share this:

  • Click to share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Click to share on X (Opens in new window) X
Join our WhatsApp Channel
NgHausa

NgHausa

Recent Posts

  • Najeriya 4–1 Gabon: Super Eagles Sun Tsallake Zuwa Wasan Karshe
  • Ba zan bari a gina filin da ba shi da takardu ba – Ministan Abuja Wike
  • Matsalar Tsaro a Kano: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Faruruwa, Sun Yi Garkuwa da Mata Biyar
  • NYSC Ta Fitar da Lambobin Kira Ga Mambobin Batch C Na 2025
  • Rikicin Nyesom Wike da Sojojin Najeriya: Abin da ya faru a Abuja

Recent Comments

  1. Yusuf tanko on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”
  2. Abdulazeez jibrin on Yadda Zaka Samu Tallafin Kudi a Najeriya (2025): Matakai da Sharuɗɗa
  3. Bashir Gamzaki on COMPLETE RAMADAN TAFSEER 1446/2025 PROF. Isah Ali Ibrahim Pantami
  4. IBB on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”
  5. IBB on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”

Archives

  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024

Categories

  • Blog
  • Entertainment
  • Hausa Series
  • KannyWood
  • Labaran Duniya
  • Lafiya
  • Nigeria
  • Nishadi
  • Opportunity
  • Siyasa
  • Sports
  • TAFSEER
  • Wasanni
NgHausa News

© NG Hausa News – 2025

Navigate Site

  • About Us
  • Privacy Policy
  • Terms and Conditions
  • Disclaimer
  • Contact Us

Follow Us

No Result
View All Result
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood

© NG Hausa News – 2025

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
Enable Notifications OK No thanks