Hamdiyya Sidi Shariff da Lauyanta na Fuskantar Barazana a Najeriya

Ƙungiyar Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gudanar da bincike mai zurfi tare da tabbatar da kare lafiyar Hamdiyya Sidi Shariff da lauyanta, Abba Hikima, daga duk wata barazana da ka iya shafar rayuwarsu.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na Najeriya, Isa Sanusi, ya fitar, ya bayyana cewa, “yanzu haka, bayan fuskantar shari’a saboda amfani da ƴancinta na tofa albarkacin baki, Hamdiyya Sidi Shariff da lauyanta, Abba Hikima, suna fuskantar barazana daga wasu ɓatagari da ke kiran kansu ‘jami’an sirri,’ ta hanyar kiraye-kirayen waya da kuma yi musu barazana a fili.”
Sanarwar ta ƙara da cewa lauyanta ya nemi kariya daga ƴan sanda yayin zaman kotun da aka yi kwanan nan, saboda fargabar tsaron lafiyarsu. Wannan yanayi, in ji sanarwar, ya sa zuwansu kotun ke kasancewa cikin wahala.
Hamdiyya Sidi Shariff tana fuskantar shari’a ne saboda zargin ɓata sunan gwamnan jihar Sokoto, wani lamari da ya ja hankalin al’umma da dama.