Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin ‘ƙauyawa’ a jihar Kano

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta haramta bukukuwan “Ƙauyawa.” Wannan su ne irin bukukuwan da matasa ke yi, inda ake tara jama’a, a yi rawa, a saka waƙa da sauti mai ƙarfi. Sau da yawa irin waɗannan bukukuwa suna janyo hayaniya, tayar da hankali, da kuma halayen da ba su dace ba.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce sun dauki wannan mataki ne don kare tarbiyyar jama’a. Ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka yi a yau Asabar. Ya ce gwamnati tana son al’umma su zauna lafiya, su bi doka, kuma su guji abubuwan da ke da illa ga tarbiyya.
Ba wai bukukuwan “Ƙauyawa” kawai aka dakatar ba, har da duk inda ake gudanar da su. Misali, idan wani yana da event center inda ake yi wa mutane haya don shirya biki, ba zai sake ba da wurin don irin wannan biki ba — har sai gwamnati ta bada sabon umarni.
Sabuwar dokar da aka fitar ta bai wa hukumar ikon kula da DJs da wuraren bukukuwa. DJs su ne masu saka waƙa a biki. Idan DJ ya taka waƙa a irin wannan biki da aka haramta, shima ya karya doka.
Duk wanda ya shirya biki da sunan “Ƙauyawa,” ya aikata laifi.
El-Mustapha ya roƙi shugabannin al’umma da jami’an tsaro su taimaka wajen aiwatar da wannan doka. Ya ce Hisbah, ƴan sanda, da ƴan bijilanti su sa ido don ganin ba a ci gaba da shirya irin waɗannan bukukuwa ba.