Hausa Series

Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano Ta Dakatar da Fim ɗin Zarmalulu

Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu, tare da gayyatar dukkannin waɗanda suka fito a cikinsa domin jin ba’asi. Wannan mataki ya biyo bayan zargin cewa an yi amfani da kalmar da ba ta dace ba a matsayin sunan fim ɗin.

Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa sun karɓi korafi daga wasu ƴan kishin Kano dangane da fim ɗin, bisa zargin cewa ba shi da ingantacciyar ma’ana. Bisa haka ne hukumar ta yanke hukuncin dakatar da fim ɗin tare da gayyatar masu ruwa da tsaki domin jin ta bakinsu.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, hukumar ta jaddada cewa tana da ikon dakatar da duk wani fim da ba ta gamsu da yadda aka shirya shi ba. Haka kuma, za a ladabtar da duk wanda aka samu da aikata abin da bai dace ba a cikin kowanne fim.

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta daɗe tana sa ido kan ingancin fina-finai domin tabbatar da cewa ana bin ƙa’idoji masu dacewa da al’adu da dokokin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button