Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, karkashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta dakatar da wasu jarumai mata uku da kuma mawaki Usman Soja Boy. Wannan hukunci ya biyo bayan zarge-zargen rashin da’a, batsa, da kuma sanya tsiraici a bidiyoyin da suka wallafa a kafafen sada zumunta.
Sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana ta ce an haramta tace duk fina-finai ko waฦoฦin da waษannan jaruman suka fito a ciki.
- SAMHA M. INUWA
Hukumar ta dakatar da jaruma Samha M. Inuwa na tsawon shekara guda bisa dalilan da suka haษa da:
Sanya tufafin da suka saba tarbiyya.
Wallafa bidiyoyin da ke nuna tsiraici.
Rahotanni sun nuna cewa jarumar ta sha gargaษi daga hukumar kan irin halayenta, amma ta ฦi gyara. Bidiyon da ya jawo matsala ya nuna tana sanye da tufafi masu bayyana surar jikinta, wanda hakan ya haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a.
- USMAN SOJA BOY
Hukumar ta dakatar da mawakin Kannywood, Usman Soja Boy, bisa dalilin wallafa bidiyoyi masu ษauke da batsa. Sanarwa ta nuna cewa:
An kwace lasisinsa na aiki a Kannywood.
An haramta tace fina-finai ko waฦoฦin da ya fito a ciki.
Duk da haka, mawakin ya yi ikirarin cewa dakatarwar ba ta dame shi ba, yana mai cewa shi ne ya fi taimakawa masana’antar, ba akasin haka ba.
- WASU JARUMAI MATA BIYU
Baya ga Samha M. Inuwa da Usman Soja Boy, wasu jarumai mata biyu da suka fito a cikin bidiyoyin mawakin sun haษu da hukuncin dakatarwa. Duk da haka, babu cikakken bayani a kan sunayensu ko irin laifukan da suka aikata, amma hukumar ta tabbatar da cewa sun karya dokokin tace fina-finai.

















