KannyWood

Rashinsa: Tasirin Rabilu Musa Ibro a Kannywood

Duk da ya bar duniya shekaru 10 da suka wuce, har yanzu Rabilu Musa Ibro yana daga cikin taurarin finafinan Kannywood da suka shahara wajen nishaɗantar da jama’a da kuma burge masu kallo.

Har yanzu, ƙananan bidiyon finafinansa na yawo sosai a shafukan sada zumunta, irin su Facebook da Tiktok.

Ya dai zama wani irin Mahadi mai zamaninsa – aƙalla a duniyar Kannywood.

Gwanintarsa, hazaƙarsa, da kuma ƙwarewarsa wajen sarrafa harshe, nuna al’adun gargajiyar Bahaushe, da amfani da sauƙaƙan salo wajen aika saƙo, sun ƙara ɗanɗano da armashi ga finafinansa da ake shirya su da ƙaramin kuɗi.

Ya kai kololuwar shahararsa musamman a wajen masu son finafinan da ke caccakar “rayuwar ƙarya ta ‘yan birni” da kuma “raye-rayen ‘yan mata masu ɗammammun tufafi” a kan titi.

Saurin fitar da finafinansa masu salo na musamman, inda mafi yawan su ke ɗauke da tambarin sunansa – kamar Ibro Angon Hajiya, Andamali, Na-Mamajo, Ibro Ɗan Almajiri, Ibro Ya Auri Baturiya, Ibro Ɗan Fulani, Ibro Ɗan Zaki, Ibro Ɗan Siyasa, da Ibro Police – ya sa suka mamaye kasuwa cikin sauƙi.

Da wuya a iya sanin yawan finafinan da Rabilu Musa Ibro ya shirya.

Yana kan kololuwar sharafinsa lokacin da mutuwa ta riske shi a ranar Laraba, 10 ga watan Disamba, 2014.

Ɗan Ibro ya yi matuƙar fice a finafinan barkwanci na Kannywood, wanda aka fi sani da Camama, ko da yake daga bisani ya shiga finafinai masu ɗaukar salon Sentimental.

Sai dai, kamar yadda Hausawa ke cewa: “Ba rabo da gwani ba, mai da kamar sa.”

Tun bayan rasuwarsa, mutane da dama sun fara tunanin wanda zai iya maye gurbin babban matsayinsa wajen nishaɗantar da jama’a, raya al’adun gargajiya na Bahaushe, da isar da saƙo cikin sauƙaƙan salo da iya yanko magana irin ta Ɗan Ibro.

“Kullum ji nake kamar yau Ibro ya rasu,” in ji Daushe a lokacin da yake bayyana irin alaƙar da ke tsakaninsa da marigayi Alhaji Rabilu Musa Ibro.

Alhaji Rabiu Ibrahim Daushe, wanda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu shirya finafinan barkwanci tare da Ibro, ya bayyana wa BBC cewa, a ganinsa, babu wanda zai iya cike gurbin da Ibro ya bari a Kannywood.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button