Dawowar Tsofaffin Jaruman Kannywood: Yadda Finafinai Masu Dogon Zango Suka Farfaɗo da Su

Har yanzu akwai jaruman Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu tun bayan da masana’antar ta shiga matsin tattalin arziƙi, wanda ya rage yawan shirya fina-finai. Rashin kasuwanci ya tilasta wa masu shirya fina-finai komawa wasu harkoki domin samun rufin asiri.
A tsakiyar wannan hali ne aka buɗe sinima a Ado Bayero Mall, inda furodusoshi suka gwada sabuwar hanya domin farfaɗo da masana’antar. Sai dai hakan bai yi tasiri sosai ba, har sai da aka koma dora finafinai a YouTube, wanda ya taimaka wajen dawo da martabar Kannywood.
A sakamakon hakan, masana’antar ta fara farfaɗowa, har ta kai ga dawowar wasu tsofaffin jarumai ta hanyar finafinai masu dogon zango. Daga cikin jaruman da suka koma fagen fama akwai:
1. Hadiza Kabara
Hadiza Kabara ta kasance cikin jaruman farko-farko mata a Kannywood. A farkon shigarta masana’antar, ta riƙa fitowa a matsayin budurwa tare da jarumai irinsu Musbahu Ahmad, Saima Muhammad da Fati Muhammad.
Bayan wani lokaci, ta ɓace daga masana’antar, sai dai finafinai masu dogon zango sun dawo da ita. Ta taka muhimmiyar rawa a shirin Daɗin Kowa na Arewa24, inda ta fito a matsayin “Lantana mai adashe”. Haka kuma, tana daga manyan taurari a Gidan Badamasi, inda take takawa a matsayin “Hauwa Alhaji Badamasi”.
2. Bashir Bala Chiroki
Bashir Bala Chiroki ya shahara a finafinai irinsu Sangaya, inda ya fi fitowa a matsayin mai kitsa tuggu. Ya kuma yi suna a matsayin jarumin barkwanci a Kannywood.
Sai dai daga baya an daina ganinsa a fim, har ya kai ga komawa tallan kunun aya saboda rashin gayyatarsa a finafinai. Amma shirin ‘Gidan Sarauta’ na Abubakar Bashir Maishadda ya dawo da shi cikin masana’antar, inda ya fito a matsayin wani bafade mai ban dariya.
3. Mustapha Musty
Mustapha Musty na daga cikin jaruman da suka ja zare a shekarun 2000, inda yakan taka rawar tallafawa manyan jarumai, ko kuma fitowa a matsayin babban jarumi.
Bayan wani lokaci ya ɓuya daga masana’antar, amma finafinai masu dogon zango suka dawo da shi. Yanzu yana taka rawa a shirin Kwana Casa’in na Arewa24 da kuma Garwashi na UK Entertainment.
4. Magaji Mijinyawa
Magaji Mijinyawa ya shahara wajen fitowa a matsayin iyayen gida a finafinai. Ya kasance ɗaya daga cikin tsofaffin jaruman Kannywood masu ƙwarewa.
Bayan wani lokaci ba a jinsa, sai da Gidan Badamasi ya dawo da shi a matsayin “Alhaji Badamasi”, wani attajiri mai matuƙar rowa da kwadayin kuɗi.
5. Nura Dandolo
Nura Dandolo ya fara shahara ne ta hanyar finafinan barkwanci tare da marigayi Rabilu Musa Ibro. Sai dai daga baya ya ɓuya, har mutane suka fara tunanin ya bar Kannywood gaba ɗaya.
Yanzu ya dawo cikin Gidan Badamasi, inda yake taka rawar Yaya Ɗankwambo, ɗan Alhaji Badamasi, kuma yana daga cikin jaruman da suka fi jan hankalin masu kallo.
6. Lawan Ahmad
Lawan Ahmad ya daɗe a Kannywood, sai dai shigowar matasan jarumai ya jefa shi baya, har ya koma siyasa. Sai dai fim ɗinsa na Izzar So ya dawo da shi fagen fim, inda ya zama daya daga cikin fitattun jaruman finafinai masu dogon zango a YouTube.
7. Tijjani Asase
Tijjani Asase ya yi suna a Kannywood, amma daga baya ya yi nesa da fim. Sai da fim ɗin A Duniya ya dawo da shi, wanda ya canza yanayin dabanci a finafinai. Yanzu yana fitowa a finafinai irin su Ɗan Jarida da wasu.
8. Tijjani Faraga
Tijjani Faraga ya fara fim tun ana shirya finafinai a Jos, amma daga baya ya yi nesa da masana’antar. Sai dai finafinai irinsu Labarina da Manyan Mata suka dawo da shi, inda ya ƙara haskawa sosai.
9. Isah Ferozkhan
Isah Ferozkhan, wanda aka fi sani da Presido, ya daɗe a masana’antar. Sai dai shirin Labarina mai dogon zango ne ya dawo da shi. Har wa yau, yana cikin taurarin finafinai kamar Manyan Mata da Garwashi.
10. Shuaibu Lawal
Shuaibu Lawal ya daɗe yana fitowa a finafinai, musamman na dabanci. Sai dai yanzu finafinai irinsu A Duniya, Ɗan Jarida da Manyan Mata suka dawo da shi cikin masana’antar.
Har wa yau, akwai wasu jarumai da suka fara dawowa, irin su:
- Zahradden – Ya dawo da fim ɗin Labarina
- Auwal Isa West
- Ramadan Booth
- Teema Makamashi
- Rahama MK – Ta fito a fim ɗin Kwana 90
- Sauran jaruman da suka fara dawowa cikin finafinan zamani.
Tare da ci gaban finafinai masu dogon zango, masana’antar Kannywood na samun farfaɗowa, kuma ana fatan dawowar wasu tsofaffin jarumai domin ƙara wa masana’antar ƙayatarwa.