Siyasa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, Ya Tabbatar da Ficewarsa Daga APC, Ya Koma SDP

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ba da sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin ƙasa, inda ya kuma bayyana cewa ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Hakan ya kawo ƙarshen jita-jitar da ta yi taɗi kan inda tsohon gwamnan zai nufa bayan rabuwarsa da jam’iyyar APC.

A ranar Litinin, El-Rufa’i ya wallafa wannan sanarwar a shafukansa na sada zumunta, inda ya bayyana cewa: “Yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), kuma zan ci gaba da tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba.”

Bayan haka, tsohon gwamnan ya ziyarci ofishin jam’iyyar SDP, inda ya yanka katin zama ɗan jam’iyya.

A cikin wata hira da kafar talabijin ta Arise TV kwanakin baya, El-Rufa’i ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta kau da kai daga manufofin da aka kafa ta a kai. Ya kuma yi zargin cewa jam’iyyar ta gaza gudanar da taron shugabanninta na ƙasa tsawon shekaru, wanda ya saba wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani kan lamarin…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button