Labaran Duniya

EFCC ta kama Murja Kunya saboda zarginta da ‘wulaƙanta takardun naira’

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sanar da kama fitacciyar ƴar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, bisa zargin wulaƙanta takardun kuɗin Najeriya, wato naira.

A wata sanarwa da ofishin shiyya na hukumar da ke Kano ya fitar, an bayyana cewa an kama Murja ne sakamakon aikata laifin da ake zarginta da shi.

“An kama Murja Kunya ne bisa zargin wulaƙanta takardun kuɗin naira a yayin da take zaune a otal ɗin Tahir Guest Palace da ke Kano. Wannan kama ta na zuwa ne bayan da ta tsere daga belin da aka ba ta kimanin wata guda da ya gabata.”

Tun da farko, hukumar EFCC ta kama Murja a watan Janairu na 2025, bayan ta karya dokar babban bankin Najeriya (CBN) da ke hana wulaƙanta kuɗin ƙasa. Bayan kama ta a wancan lokaci, an ba ta beli tare da shirin gurfanar da ita a gaban kotu a Kano. Amma da lokacin shari’ar ta yi, sai aka neme ta aka rasa.

Bayan makonni ana nemanta, jami’an EFCC sun sake kama ta a ranar Lahadi, 16 ga watan Maris, sannan aka mayar da ita ofishin hukumar da ke Kano.

Sanarwar hukumar ta ƙara da cewa ana shirye-shiryen gurfanar da ita a gaban kotu domin fuskantar tuhuma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button