Nishadi
Jamila labarina Ta Bayyana: “Ni Ban Da Alaƙa Da Gidan Sarauta”

“Ni ban da wata alaƙa da gidan sarauta, ko ma abokantaka ba na da ita da gidan sarauta,” in ji Jamila a cikin shirin Labarina.
Ta bayyana hakan ne a yayin da take hira a shirin Dausayin Kannywood na Kanawa Radio, inda aka tattauna kan rayuwarta da yadda ta shigo harkar fim.
Fatima Ko kuma in ce Jamila Labarina ta kara da cewa, fim ba wai sai kana da alaƙa da wani ko wani gida ake saka ka a ciki ba.
A cewarta, abu mafi muhimmanci shi ne darakta ya ga cewa zaka dace da wani bangare, sannan ka iya bashi abinda yake bukata a wajen aiki.
Shin, me kuke ganin gaskiya ce a wannan magana nata?