JARUMA MARYAM YAHAYA TA SIYA SABON MOTA

JARUMAR KANNYWOOD TA ƁARE SABUWAR MOTA TA KIMANIN N50M
Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Maryam Yahaya, ta sayi sabuwar motar Marsandi da ake tsammanin ta kai kimanin Naira miliyan 50.
Jarumar ta wallafa hotunan motar a shafukanta na kafafen sada zumunta, inda masoya da masu fatan alheri suka yi mata rubdugu da taya ta murnar wannan abin alheri.
Maryam Yahaya ta godewa Allah (SWT) a cikin sakonta, inda ta ce:
“Godiya ta tabbata ga Allah.”
Shafin Kannywood Empire ya wallafa labarin cewa:
“Masha Allah, Jaruma Maryam Yahaya ta mallaki dankareriyar Mercedes Benz ta kusan Naira miliyan 50, Allah ya sanya alheri.”
Masoya sun yi mata rubdugu, inda wasu suka ce:
- Umar Abubakar Nafson Guy: “Allah ya sanya alheri ƴa kauda idon maƙiya.”
- King Mahdi: “Ah ah ah Maryama ina taya ki murna, Allah ya sa albarka ya karo dubunsu.”
- Umar Usman: “Masha Allah muna taya ki murna, Allah ya tsare ya sa a kashe lafiya.”
Labarin ya nuna farin cikin da masoya ke yi wa jarumar saboda nasarar da ta samu.