KannyWood

Kannywood: Masana Na Tunanin Komawa Gidajen Gala Bayan Dogaro da YouTube

A daidai lokacin da ake ƙoƙarin inganta harkokin kasuwancin finafinan Kannywood, masana da masu ruwa da tsaki a masana’antar suna fara waiwayen hanyoyin da aka bi a baya domin gano sabbin dabarun da za su ƙara mata tagomashi da riba mai ɗorewa.

A yau, yawancin masu shirya finafinai sun karkata ne zuwa manhajar YouTube, inda ake kallon finafinai kai tsaye kuma masu shirya sukan samu kuɗin shiga ta hanyar tallace-tallace. Wannan ya sauya tsarin da aka saba a da, lokacin da CD ke jagorantar kasuwa kafin fasahar zamani ta kawar da ita gaba ɗaya.

Bayan rugujewar kasuwancin CD, masana’antar ta shiga wani yanayi na fargaba, inda da yawa daga cikin furodusoshi suka ja gefe saboda rashin kasuwa. Sai dai daga baya an ga alamun farfaɗowa lokacin da aka fara amfani da sinima domin haska finafinai. Amma duk da kyakkyawan shirin, yawanci ba a cika samun riba yadda ake fata ba.

See also  Maishadda: “Burin da nake da shi yanzu shi ne na fitar da Kannywood zuwa duniya!”

Da rashin nasarar tsarin sinima, masana suka sake komawa gida wajen nazarin yadda za su dawo da martabar harkar. A cikin wannan tunani ne aka sake komawa YouTube, wanda ya zama babbar hanya ta samun kallo da riba. Sai dai masana sun fara tambayar: Shin dogaro da YouTube kaɗai zai wadatar?

Sabon Tunanin Komawa Gidajen Gala

Wasu masana suna ganin lokaci ya yi da za a sake farfaɗo da tsoffin gidajen gala, wato wuraren da ake haska finafinai kai tsaye a gaban jama’a. Malamin jami’a a Jami’ar Cologne da ke Jamus, kuma mai sharhi kan harkokin finafinai, Dokta Muhsin Ibrahim, ya bayyana cewa wannan mataki zai iya zama babban ci gaba.

A cewarsa:

“Tun a da akwai ƙananan gidajen kallo da ake nuna finafinai, musamman na Kannywood. Idan an dawo da wannan salo, zai taimaka wajen bunƙasa masana’antar. Dogaro da YouTube kaɗai na da hatsari saboda tsarin kamfanin na iya sauyawa a kowane lokaci.”

Ya ƙara da cewa duk wata hanya da za ta ƙara ribar masana’antar — ko ta zama ƙari ga YouTube — abu ne mai kyau da ya dace a runguma.

See also  ALI NUHU YA GARGADI RAYYA KWANA CASA'IN KAN SHIRIN ZANA TATTOO

Ra’ayin Furodusa Nazir Auwal (Ɗanhajiya)

A nasa ɓangaren, shahararren furodusa Nazir Auwal (Ɗanhajiya) ya bayyana cewa komawa haska finafinai a gidajen gala abu ne mai wahalar gaske a yanzu.

Ya ce:

“A baya kafin fim masu dogon zango su shigo, muna shirya finafinai sannan mu kai a kalla a gidajen dirama. Amma yanzu lokaci ya canja, kuma yawanci ana yin finafinan series ne. Wannan ya sa ba zai zama da sauƙi a dawo amfani da gidan dirama wajen haska finafinai ba.”

Duk da haka, ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Kannywood da gidajen gala, inda yawanci masana’antar ke ɗaukar ƙwararrun masu rawa daga wuraren nan idan ana buƙata.

See also  Hadizan Saima Ta Ba da Aminci Kan Abubuwan Da Ke Saka Ta Farin Ciki

Asalin Gidajen Gala

Gidajen gala ko gidajen dirama sun kasance wani tsohon salo na nishaɗi a ƙasar Hausa. A nan ne mutane ke taruwa domin kallon dirama, rawa ko wasan kwaikwayo.

Daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, Shuaibu Lilisco, shi ne ya fara farfaɗo da tsarin gidan gala, bayan ya gaji salon tsoffin gidajen dirama da kuma rawar ƙoroso. A hankali wannan tsarin ya bazu a arewacin Najeriya, kafin daga bisani ya tsallaka zuwa wasu sassan ƙasar da ma ƙasashen Afirka ta Kudu.

Yanzu haka ana ganin cewa idan aka tsara tsarin da kyau, komawa haska finafinai a gidajen gala na iya zama sabon babi da zai ƙara wa Kannywood armashi da riba mai ɗorewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks