Masana’antar Kannywood ta shiga cikin jimami bayan samun labarin rasuwar shahararren jarumi Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala, bayan doguwar jinya da ciwon daji a yau Lahadi, 2 ga Nuwamba, 2025.
Marigayi Malam Nata’ala ya shahara a cikin shirin Dadin Kowa, inda ya taka rawar gani da halayen nishadantarwa da ilmantarwa. Tun kafin rasuwarsa, jarumin ya daɗe yana fama da rashin lafiya, yana kuma neman taimakon jama’a domin samun lafiya.
A lokacin jinyarsa, Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗauki nauyin kula da lafiyarsa, haka kuma Shugaban ƙasar Nijar ya taimaka masa da kuɗi don ci gaba da magani. Duk da wannan taimako, cutar ta ci gaba da galaba a kansa har Allah Ya yi masa rasuwa.
Masana’antar Kannywood da masoyansa sun shiga cikin alhini da kuka, yayin da mutane ke bayyana ta’aziyyarsu a shafukan sada zumunta. Wata fitacciyar marubuciya ma ta tura sakon ta’aziyya tana roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya kuma saka shi a Aljanna Firdausi.
Malam Nata’ala ya kasance mutum mai barkwanci, hazaka da kyakkyawan hali. Zai bar gagarumar tazara a masana’antar Kannywood da zukatan masoyansa.
Allah Ya jikansa Malam Nata’ala. Ameen.













