KannyWood

Ko kunsan cewa A Yanzu ba Film din da aka fi kallo Kamar Jamilun Jidda

Idan ka cire korafin da masu kallo suka yi game da rawar da Jidda ta taka, za ka ga cewa a wannan shekarar, an yi wani Series mai kyau da tasiri na Jamilun Jidda. Labarin ya kasance mai kyan gani, kuma idan ba a karya shi ba nan gaba, zai ci gaba da zama abin tunawa.

Ko da yake idan ka kalla film ɗin, za ka ga kamar akwai haɗe-haɗe da wasu fina-finan Kannywood, irin su Tsakaninmu da Jamilun Jidda na Ali Nuhu da Rahama Hassan. Duk da haka, ba za ka iya musun kyawun tsarinsa da kuma tsaruwarsa ba.

Misali, kamar yadda ya faru a shekarar 1975 a masana’antar Bollywood, babu wani fim da aka fi kallo kamar Sholay. Ko da yake fim ɗin ya sami lambar yabo ta Filmfare, ba a musanta cewa ya samo kwaso daga wasu fina-finan Bollywood da Hollywood, irin su Once Upon A Time In The West, Seven Samurai, Mera Gaon Mera Desh, da The Magnificent Seven.

Labari ne ke kira ’yan wasa, amma ba a buƙatar cewa jarumai su ƙware a kowane fanni. Maimakon haka, ya kamata furodusoshi su daina gaggawar tafiya location, su ba da lokaci na koyar da jarumai abubuwan da ba su saba ba, domin su iya taka rawar da ake buƙata.

Abu ne na yau da kullun cewa duk wani fim mai kyau, masu sukar fina-finai za su yi nazarinsa, ko da bayan shekaru. Misali, babu wani fim da ya yi tasiri kamar Squid Game, amma duk da haka, masu suka sun yi nazarinsa kuma sun ba da shawarwari don ingantawa. Ba wani daga cikin furodusoshi da ya ce ana yi masa hassada saboda haka.

Ya kamata ’yan masana’antar Kannywood su yi godiya da Allah da aka dawo da hankalin masu kallo a kansu. Don haka, su karɓi gyara da kyau, su daina fushi idan aka yi musu sukar aiki. Wannan yana nuna cewa ana kallon aikinsu ne da kyau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button